Rashawa: Kotu ta dage sauraron karar Jonah Jang har zuwa 27 ga watan Yuni

Rashawa: Kotu ta dage sauraron karar Jonah Jang har zuwa 27 ga watan Yuni

-Kotun jihar Filato ta dage karar tsohon gwamnan jihar zuwa 27 ga watan Yuni bayan an kwashe tsawon lokaci ana muhawara tsakanin bangaren kariya da kuma masu kara

-Daniel Longji alkalin kotun ne ya dage wannan karar inda ya ce za'a cigaba da sauraron karar ranar Alhamis 27 ga watan Yunin 2019

Babbar kotun jihar Filato wacce ke Jos a ranar Alhamis ta dage sauraron karar tsohon gwamnan jihar Filato sanata Jonah Jang wanda ake zargi da almundahanar kudin da yawansu ya kai naira biliyan 6.3.

Idan baku manta ba wannan badakkala ta dade a gaban kotun ta Filato inda ake tuhumar Jang da wawushe biliyoyin kudade na gwamnati.

Jang wanda tsohon dan takarar shugabancin kasar nan ne karkashin jam’iyar PDP, yana fuskantar tuhuma tare da ma’ajin ofishin sakataren gwamnatin jihar Filato, Yusuf Gyang Pam daga wurin hukumar EFCC.

Yayin zaman kotun na ranar Alhamis, Mista Jonah Kpar, wanda yake matsayin shaida daga bangaren EFCC yayi kokarin bayar da wani daftari wanda aka samu daga majalisar zartarwar jihar Filato a matsayin shaida ga kotu.

Sai dai kuma, Mike Ozekhome wanda ke kariyar Jang yaki amincewa da wannan abu inda yake cewa: “ Irin wadannan jawabai ne na sirri wanda bayyanasu a bainar jama’a kan iya haifar da babbar matsala ga gwamnati.”

Har ila yau, lauyan EFCC, Rotimi Jacob yayin da yake martani a kan batun cewa ya yi: “ Wadannan takardun za suyi wa kotu amfani wajen warware wannan badakkala. Kuma za’ayi amfani dasu ne kawai a kotu ba wai waje zasu fita ba wurin jama’ar gari.”

Bayan da alkali ya gama sauraren muhawara daga bangarorin biyu, Daniel Longji ya dage karar zuwa ranar Alhamis 27 ga watan Yunin 2019, domin sanin ko kotu zata karbi wadannan takardu ko kuma ba zata karba ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel