Rikicin Ganduje da Sanusi: Babban basarake a kudu ya ziyarci Obasanjo

Rikicin Ganduje da Sanusi: Babban basarake a kudu ya ziyarci Obasanjo

- Mai rike da mukamin 'dein' na masarautar jihar Delta, mai martaba Benjamin Ikenchukwu (Keagborekuzi I), ya gana da Obasanjo a kan rikicin da ke tsakanin gwamna Ganduje da Sarki Sanusi

- Dein Ikenchukwu ya ce ya shiga batun maganar fadar Kano da gwamnatin jihar ne domin kawo sulhu, saboda Najeriya na bukatar kwanciyar hankali a wannan lokaci

- Basaraken ya bayyana dalilinsa na tuntunar Obasanjo domin ya saka baki a cikin rikicin masarautar Kano da gwamnatin jihar

- Sarkin ya yi kira ga shugaba Buhari da ya saka baki domin yin sulhu tsakanin Ganduje da Sanusi. Kazalika ya yaba wa Buhari a kan sake nada Godwin Emefiele a matsayin gwamnan CBN

Saboda damuwar da ya yi da rikicin da ke faruwa tsakanin masarautar Kano da gwamnatin jihar, mai rike da mukamin 'dein' na masarautar jihar Delta, mai martaba Benjamin Ikenchukwu (Keagborekuzi I), ya gana da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, a kan rikicin da ke tsakanin gwamna Ganduje da Sarki Sanusi II.

An yi ganawar ne tsakanin basaraken da Obasanjo a garin Abeokuta a jihar Ogun domin tattauna yadda za a yi sulhu tsakanin gwamna Ganduje da sarki Sanusi.

Dein Ikenchukwu, wanda ya ziyarci Obasanjo bayan dawowarsa daga karbar wata sarauta da aja bashi a kasar Benin, ya lashi takobin gana wa da shugaba Buhari a kan batun Ganduje da Sanusi.

DUBA WANNAN: Zan taimaki kasar Sahrawi ta samu 'yancin kai - Buhari

Da yake bayyana dalilinsa na gana wa da Obasanjo domin ya yi sulhu tsakanin Ganduje da Sanusi, Basaraken ya ce tsohon shugaban kasar na da gogewa a kan sanin bukatu da matsalolin 'yan Najeriya na kudu da arewa.

Kazalika ya bayyana cewar Najeriya na bukatar kwanciyar hankali a wannan lokaci, tare da bayyana cewar zai gana da gwamnoni domin su saka baki don a samu a warware matsalar da ta shiga tsakanin sarki Sanusi II da gwamna Ganduje.

Kazalika, ya yaba wa shugaba Buhari bisa sake nada Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin kasa (CBN) a karo na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel