Duniya sabuwa: Sabon jirgin kasa ya isa garin Ibadan

Duniya sabuwa: Sabon jirgin kasa ya isa garin Ibadan

-Ana cike da murna a garin Ibadan sakamakon saukar da sabon jirgin kasa da akayi

-Shugaban hukumar kula da jirgin kasa ta Najeriya ya nuna farin cikinsa game da aikin da ke gudana na jirgin kasa a garin Ibadan

Ana cike da murna a garin Ibadan sakamakon isowar jirgin kasa garin Ologuneru a Ibadan babban birnin jihar Oyo mai tsawon kilomita 152.

Shugaban hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya Alhaji Ibrahim Hassan yace za a ida sauran kilomita biyar din da ta rage daga nan zuwa karshen wannan watan na Yuni.

Alhassan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da yan kwangila da sauran masu ruwa da tsaki a farfajiyar aikin jirgin kasan a garin Ologuneru bayan da ya duba aikin tun daga garin Iju na jihar Legas.

Ya ce za a sanya layin jirgin kasa guda biyu na zauwa da na dawo wa mai kimanin tsawon kilomita 133 daga nan zuwa watan Yuli na wannan shekarar.

Ya kara da cewa bayan an gama sanya layukan ne za a dukufa wajen ganin an samar da sauran abubuwa kamar su tashar jirgin kasan.

Ya ce za a gama gina kananan tashoshin jirgin kasan tsakanin Legas zuwa Ibadan kuma za a gama ginin daga nan zuwa karshen wanna shekarar domin fara sufurin matafiya.

KARANTA WANNAN: Mutane 1,234 aka hukunta cikin shekara hudu – EFCC

Ya ce "Ana aiki a dukkanin tashoshin jirgin kasa. Idan kana da aiki irin wannan dole sai ka fi ba wani mahimmanci, mu kuma mun zabi aikin gina titin jirgin kasan. "

"Da zarar an gama aikin wanda muna da tabbacin za a gama kafin karshen watan Yuli, to zamu maida hankali wajen gina sauran wuraren aiki na jirgin kasan".

Alhassan ya yabawa shugaban kasa wajen kokarin sa na samar da ingantattun jiragen kasa a fadin kasannan.

Ya kuma jin jina ma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, wanda ya jajirce wajen ganin an samu canji ta fannin sufurin jirgin kasa.

Ya bayyana cewa dalilin da yasa aka samu tsaiko a aikin da ke gudana a Legas, na da alaka da wasu matsaloli da suke fuskanta.

Ya bayyana cewa matsalolin sun hada da gine ginen da akayi ba a bisa ka'ida ba, bututun man fetur da na ruwa da kuma wayoyin wutar lantarki da ke kan hanyar.

Shugaban hukumar ya bada albishir din cewa daga nan zuwa karshen wannan watan za a samu karin kawunan jirgin kasa guda biyu don a hada da wayanda ke kasa don fara suifurin matafiya.

Yace za a fara sufurin cikin watan Agusta kuma hukumar ta tanaji wuraren da zata rika siyar da tikitin jirgin.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel