Jawabin Buhari cike yake karyar abubuwan da ba’ayi ba – PDP

Jawabin Buhari cike yake karyar abubuwan da ba’ayi ba – PDP

-Sakataren yada labaran jam'iyar PDP ya ce babu wani abin kaiwa gida a cikin jawabin Shugaba Buhari na Ranar Dimukouradiyya.

-Kola ya sake cewa a maimakon shugaban ya maida hankali kan abubuwan dake damun al'ummar Najeriya a yau sai kuma ya dauki wanin salon na daban.

Jam’iyar PDP ta ce jawabin Shugaba Buhari na Ranar Dimokuradiyya cike yake da karyar ayyukan da ba’a aikata ba.

PDP wacce ta fitar da jawabi ta bakin sakataren yada labaran jam’iyar wato Kola Ologbondiyan ta ce: “ shugaban kasan bai da abinda zai fada wa jama’a dangane da kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma rikicin yan bindiga dake addabar sassa da daman a kasar nan.”

KU KARANTA:INEC zata hada kai da Majalisar dokoki ta domin yi wa tsarin zabe garanbawul

Jam’iyar ta cigaba da cewa: “ Abin takaicine a rana irin wannan a ce shugaban kasa bai da abinda zai ce da jama’a face ya fake da karyar ayyukan da bai yi ba. A maimakon rarrashin al’umma wacce a da ke cikin walwala da jindadi yanzu kuma abubuwan sun sauya, sai ya buge da fadan abinda ba gaskiya bane.”

“ Me zai sa wannan gwamnatin ta haqiqance lallai sai anyi bikin ranar dimokuradiyya bayan tana sane akwai matsaloli da dama a tattare da ita, wadanda suka hada da saba kundin tsarin mulki, magudin zabe, muzgunawa yan adawa da dai sauran su.

“ Abin na da ban haushi idan muka tuna cewa magudin zabe irin wanda APC keyi a yau ne aka yiwa Cif MKO Abiola a ranar 12 ga watan Yunin, 1993.” A cewar PDP.

Jam’iyar ta cigaba da cewa: “ Har wa yau, abinda ke faruwa kwatankwacin irin na shekaru 26 ne da suka wuce. Zaben 23 ga watan Faburairun 2019 cike yake damagudi, wannan dalilin ne ya sa muke kotu tare da dan takararmu Atiku Abubakar domin mu tabbatar da cewa an bamu haqqinmu.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel