Yanzu Yanzu: An zabi Abaribe a matsayin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa

Yanzu Yanzu: An zabi Abaribe a matsayin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa

Sanata Enyinnaya Abaribe mai wakilatan mazabar Abia ta Kudu a matsayin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa ta 9.

Ya yi nasarar zama shugaban ne a wurin taron jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ke gudanarwa a gidan shugaban jam'iyyar, Uche Secondus a Maitama, Abuja.

Sanata Emmanuel Bwacha mai wakiltan Taraba ta Kudu ya sake zama mataimakin shugaban marasa rinjaye yayin da Sanata Philips Aduda (FCT) ya cigaba da rike mukaminsa na bulaliyar marasa rinjaye.

Ku biyo mu domin karin bayani ...

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel