Likafa ta cigaba: An nada Sarkin Kano wani muhimmin mukami a yankin yarbawa

Likafa ta cigaba: An nada Sarkin Kano wani muhimmin mukami a yankin yarbawa

Gwamnatin jahar jahar Ekiti ta sanar da nada mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II a matsayin sabon shugaban jami’ar jahar Ekiti, kamar yadda jaridar Solacebase ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wata takarda dake dauke da sa hannun matawallen masarautar Kano, Aliyu Ibrahim Ahmed daya aika ma sakataren gwamnatin jahar Ekiti ta bayyana gamsuwar mai martaba Sarki da wannan mukami, kuma ya amince.

KU KARANTA: Mummunar arangama ya yi sanadin mutuwar Sojoji 10 da yan Boko Haram 64 a tafkin Chadi

Matawallen Kano yace mai martaba Sarki Sunusi II ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin jahar Ekiti data duba dacewarsa da wannan mukami mai muhimmanci na jagorantar hukumar gudanarwar jami’ar jahar Ekiti.

Sarkin ya yi alkawarin bayar da gudunmuwa don ganin martabar jami’ar ya daukaka, kuma an samu cigaba mai daurewa a cibiyar ilimin ta yadda zata amfani al’ummar jahar dama na kasa baki daya.

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne hukumar gudanarwar jami’ar gwamnatin tarayya dake Bini, jahar Edo ta nada Sarki Sunusi a matsayin shugaban majalisar gudanarwar jami’ar, hakanan sabuwar jami’a mai zaman kanta dake jahar Kano, Skyline ta nadashi makamancin wannan mukami.

A wani labarin kuma fitaccen Malamin addinin Islama kuma jagoran darikar Tijjaniyyah, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya kai ziyarar goyon baya da sada zumunci ga mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II a fadarsa dake garin Kano.

Shehin Malamin ya kai wannan ziyara zuwa fadar Sarkin ne a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni jim kadan bayan saukarsa daga jirgi a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano bayan kammala aikin Umarah.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel