Secondus da Sanatocin PDP sun shiga gana wa ta musamman

Secondus da Sanatocin PDP sun shiga gana wa ta musamman

Kwamitin gudanar wa (NWC) na jam'iyyar PDP ya yi wata gana wa ta musamman domin zaben shugabannin marasa rinjaye a majalisar dattijai da ta wakilai.

Ana saka ran PDP zata zabi bulaliyar majalisar na bangaren marasa rinjaye a majalisun biyu da kuma shugaban mambobin majalisar da aka zaba a karkashin tutar jam'iyyar PDP.

Taron da ke kan gudana a gidan shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, ya samu halartar dukkan Sanatoci da mambobin majalisar wakilai na jam'iyyar PDP da kuma mambobin NWC.

Tun kafin kiran 'yan majalisar, NWC na PDP ya gana domin tsara yadda za a zabi shugabannin marasa rinjayen da sauran mukaman ba tare da samun matsala ba.

Akwai kyakykyawan zaton cewar jam'iyyar PDP na son bawa sanata Philiph Aduda matsayin shugaban maraa rinjaye, sannan ta bawa sanata Enyinnaya Abaribe mukamin bulaliyar majalisa na marasa rinjaye.

Ana cigaba da gudanar da taron na sirri har ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan labari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel