APC ta bukaci kotun zabe tayi watsi da karar Atiku saboda ba dan Najeriya bane

APC ta bukaci kotun zabe tayi watsi da karar Atiku saboda ba dan Najeriya bane

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC a ranar Alhamis ta bukaci kotun zaben shugaban kasa da tayi watsi da karar dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, dake kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari.

Jam'iyyar APC ta laburtawa kotu cewa ta mika wannan bukatan ne saboda tsohon shugaban kasan ba asalin dan Najeriya bane.

Atiku ya yi takarar kujerar shugaban kasa a zaben 23 ga watan Febrairu karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Lauyan APC, Lateef Fagbemi, ya yi wannan kira ne yayinda yake martani kan jawabin lauyan PDP da ta bukaci soke bukatar APC.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Larabawan Sharawi da mataimakin shugaban kasa Sudan ta kudu

Yace: "Ya mai shari'a, ina nuna rashin amincewata a kan bukatar tabbatar da cewa mai kara (Atiku Abubakar) ya cancanci yin takara. Ina nan kan baka na cewa mun bada isassun hujjoji a martaninmu."

"Dan takaran jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP tun farko bai cancanci yin takarar 23 ga Febrairu ba."

"Saboda haka, ina bukatar wannan kotun tayi watsi da bukatar mai kara saboda babu tsoka cikinta,"

APC ta jaddada cewa Atiku Abubakar ba haifaffan dan Najeriya bane. Amma lauyan Atiku, Chris Uche, ya yi mujadalan haka inda yace tarihi ya nuna cewa Atiku dan Najeriya ne, saboda haka haka kada kotu ta saurari APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel