Zan taimaki kasar Sahrawi ta samu 'yancin kai - Buhari

Zan taimaki kasar Sahrawi ta samu 'yancin kai - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada kudirin Najeriya na goyon bayan mutanen jamhuriyar dimokradiyyar Sahrawi Arab (SADR) domin ganin burinsu na zama kasa mai cin gashin kan ta ya cika.

Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da ya karbi bakuncin shugaban kasar SADR, Brahim Ghali, a fadarsa dake Abuja.

Shugaban kasar ya ce matsayin Najeriya a kan neman 'yancin kasar SADR ya yi daidai da manufar kungiyar kasashen Afrika (AU) da majalisar dinkin duniya a kan batun 'yancin kasar Sahrawi.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ne ya sanar da manema labarai bayanan ganawar da aka yi tsakanin shugaba Buhari da Barhami.

"Najeriya na tare da yunkurin kungiyar kasashen Afrika (AU) da majalisar dinkin duniya (UN) a kan nemo bakin zaren matsalar Sahrawi," a cewar Buhari .

DUBA WANNAN: EFCC ta sake gurfanar da Aliyu, tsohon gwamnan PDP

Tun da fari, shugaba Ghali ya taya shugaba Buhari murnar sake lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu da kuma kammala bikin ranar tuna wa da ranar dimokradiyya, 12 ga watan Yuni, lafiya.

Ya yaba wa kokarin gwamnatin Najeriya wajen neman 'yancin kasar SADR a lokacin mulkin Buhari na soji.

Shugaban na SADR ya ce goyon bayan Najeriya na da matukar muhimmanci wajen kubutar da kasar da jama'ar ta daga mulkin mallaka.

Najeriya ta amince da hulda da SADR a matsayin kasa mai zaman kan ta a ranar 11 ga watan Nuwamba na shekarar 1984, lokacin mulkin Buhari a kakin soji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel