Banbarakwai: Fayose ya yabi Buhari, ya kushe Obasanjo

Banbarakwai: Fayose ya yabi Buhari, ya kushe Obasanjo

Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yabawa Shugaba Muhammadu Buhari saboda karrama marigayi Cif MKO Abiola da ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993.

A shekarar da ta gabata ne Buhari ya ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar demokradiyya kuma ya bawa karrama marigayi Abiola da lambar yabo ta 'Grand Commander of the Order of the Federal Republic' (GCFR).

Ya kuma nefi afuwar iyalan Abiola a madadin gwamnatin tarayya saboda rasuwarsa yayin gwagwarmayar kwato nasarar sa.

Gwamnatin Soji karkashin Janar Ibrahim Babangida ne ta soke zaben na 1993 da 'yan Najeriya su kayi ittifaki shine zabe mafi tsafta a tarihin Najeriya.

DUBA WANNAN: Matasan Ibo sun bayar da sunan wanda suke so Buhari ya nada SGF

A ranar Laraba, shugaban kasar kuma ya canja saka sunan Abiola a filin motsa jiki na kasa da ke Abuja.

Da ya ke tsokaci kan lamarin, Fayose da ya yi amfani da shafinsa na Twitter ya yabawa Buhari sannan ya kushe Obasanjo.

"Karrama Abiola da Buhari ya yi abin kunya ne ga Obasanjo. Lamari ne mai muhimmanci a tarihin Najeriya amma girman kan Obasanjo ya hana shi karrama dan uwansa MKO Abiola duk da cewa ya daga cikin wadanda suka fi amfana da gwagwarmayar ranar June 12 na 1993. Saboda haka na yi wa Buhari jinjina," Inji Fayose.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel