Mutane 1,234 aka hukunta cikin shekara hudu – EFCC

Mutane 1,234 aka hukunta cikin shekara hudu – EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta bayyana cewar a gurfanar da akalla mutane 1.234 a kotu tun daga 2015 zuwa yanzu.

Shugaban hukumar Ibrahim Magu ne ya bayyana haka a ranar Talata, 12 ga watan Yuni.

Magu ya kara da cewa ‘yan Najeriya sun kasance cikin kangir abin da ya kira “manyan da suka kankane komai”, ta hanyar murde zabe da kuma amfani da kudaden sata domin su danne hakkin wadanda al’umma suka zaba.

Da ya ke magana a wurin Taron Yaki da Rashawa, wanda aka gudanar a Abuja, Magu ya ce a cikin 2015 an hukunta mutane 103, wasu 194 cikin 2016, sai 189 cikin 2017 sai kuma 312 a cikin 2018.

Ya kara da cewa daga watan Janairu, 2019 zuwa yau, an hukunta mutane 406, sannan an kwato dimbin dukiyoyi na bilyoyin nairori.

Shugaban na EFCC ya ce rashawa ba wai a kan tattalin arziki kawai ta yi illa ba, ya ce ta samu gindin zama wajen yakar ta’addanci.

Ya ce hujjoji bayyanannu da kuma binciken da masana suka gabatar ya tabbatar da cewa cin hanci da rashawa sun karya lagon ingancin dimokradiyya a kasar nan a cikin shekarun da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: Bamu da wata na’ura – INEC ta mayar da martani ga Atiku

Magu ya jadadda cewa EFCC ta yi rawar gani a zaben 2019, inda ta rika sa-ido ta na kama dillalan saye da sayar da kuri’u kuma ta na gurfanar da su a gaban kotu.

Ya ce jam’iyyun siyasa sun rika sayen ‘yancan masu zabe da kudi, saboda sun san ba su da wani nagartaccen tsarin ciyar da su gaba da gare su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel