EFCC ta sake gurfanar da Aliyu, tsohon gwamnan PDP

EFCC ta sake gurfanar da Aliyu, tsohon gwamnan PDP

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Neja a gaban wata kotun tarayya da ke Minna bisa zarginsa da badakalar kudin magance matsalar kwararowar hamada da yawansu ya kai biliyan N1.9.

EFCC ta gurafanar da tsohon gwamnan ne a ranar Alhamis tare da tsohon kwamishinansa na muhalli, Umar Nasko, wanda ake zargi da hada baki da Aliyu wajen yin sama da fadi da kudaden.

Hukumar EFCC ta ce laifukan da ake tuhumar tsohon gwamnan da kwamishinan sun saba da sashe na 18(a) na laifukan fitar da kudade zuwa ketare, sanann ta shaida wa kotun cewar sashe na 15(3) ya tanadi hukuncin aikata laifin.

EFCC na zargin mutanen biyu da fitar da kudaden kiyaye muhalli daga kwararowar hamada zuwa kasashen ketare.

A shekarar 2014 ne gwamnatin tarayya ta bawa jihar Neja fiye da biliyan N1.940 domin yin amfani da su wajen kiyaye kwararowar hamada.

DUBA WANNAN: Masu neman aiki sun mamaye harabar majalisa, hoto

Kamfanin dillancin labara na kasa (NAN) ta rawaito cewar an sake gurfanar da Aliyu da Nasko bayan an ma ye gurbin Jastis Yellim Bogoro, alkalin dake kula da shari'arsu, da sabon alkali, Aminu Aliyu.

Da aka karanta tuhumar da ake yi musu, wadanda ake karar sun ce basu aikata laifin ba.

Bayan lauyoyin kowanne bangare sun yi mahawara a kan bayar da belin wadanda ake tuhuma, alkalin kotun, Jastis Aminu, ya ce ya amince da hukuncin jastis Bogoro na bayar da belin Aliyu da Nasko.

Daga bisani ya daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Yuli na shekarar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel