'Yan bindiga sun sace uwargidan shugaban NLC na Taraba

'Yan bindiga sun sace uwargidan shugaban NLC na Taraba

Rundunar 'Yan sandan reshen Jihar Taraba ta tabbatar da sace Abigail Gambo, matar shugaban kungiyar kwadago (NLC) Peter Gambo da kuma Emeka Okoronkwo mai gidan burodi na 'Our Nation Bread' da ke Jalingo.

Kakakin Rundunar 'Yan sandan Jihar, David Misal ya tabbtar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) afkuwar lamarin a ranar Alhamis a Jalingo.

Mista Misal ya ce an sace mutane biyun ne a gidajen su da ke unguwar Magami a Jalingo, babban birnin jihar misalin karfe 1 na daren ranar Alhamis.

DUBA WANNAN: Mutane 7 da su kayi bakin jini saboda gwagwarmayar 'June 12'

"An tabbatar cewa an sace mutane biyu kuma an yi wa mutum daya rauni a daren ranar Alhamis a Jalingo," inji shi.

Shugaban na NLC, ya tabbatar wa 'Yan sanda afkuwar lamarin inda ya ce sun firgice kuma suka nemi wurin tsira.

A cewar sa, "sunyi awon gaba da uwar gida na bayan sunyi harbe-harbe a gidan."

Mista Gambo ya yi bayanin cewa ya mika rahoto ga 'Yan sanda kan lamarin inda ya ce har yanzu masu garkuwa da mutanen ba su tuntube shi ba.

Ya kuma ce an sace makwabcinsa, mai kamfanin burodi.

NAN ta gano cewa 'yan bindigan sun harbi mai tsaron Mista Okoronkwo yanzu haka ya na Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Jalingo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel