Bamu da wata na’ura – INEC ta mayar da martani ga Atiku

Bamu da wata na’ura – INEC ta mayar da martani ga Atiku

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta karyata batun cewa na’urar da ke dauke da sakamakon zaben Shugaban kasa na tanar 23 watan Fabrairu na a hannunta.

Hukumar INEC ta bayyana matsayarta ne a kotun zabe Shugaban kasa dake Abuja inda ake kalubalantar sakamakon zaben.

Atiku Abubakar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta hannun lauyoyinsu karkashi jagorancin Levy Uzoukwu (SAN) sun bukaci kotun zabe ta tursasa INEC basu damar duba na’urar da kuma na’urar tantance katunan zabe da aka yi amfani dasu waje gudanar da zaben.

Amma lauyan INEC, Yunus Ustaz Usman (SAN) ya nemi kotu ta yi watsi da bukatar.

“Suna bukatar mu kawo abunda bau dashi,” inji shi.

Ya ja hankalin kotun zaben ga hukuncinta na ranar 6 ga watan Maris da ya ba PDP damar duba kayayyakin zabe kawai ba tare da na’urar ba.

Lauyan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Wole Olanipekun (SAN) da na All Progressives Congress (APC), Lateef Fagnemi (SAN) sun bukaci kotun da tayi watsi da bukatar bisa rashin bayyana samuwar na’uran.

Atiku yayi ikirarin cewa sakamako daga na’urar INEC ya nuna cewa ya samu jimlan kuri’u 18,356,732 bisa kuri’u 16,741,430 da Buhari ya samu.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta dage zamanta zuwa 2 ga watan Yuli, ta kafa kwamitin mutum 12 na wucin-gadi

INEC ta sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe zabe ta hanyar tattara sakamakon zabe na hannu inda ya samu kuri’u 15,191,847 sannan Atiku ya samu kuri’u 11, 262,978.

Daga cikin wadanda suka shaida zaman kotun akwai dan takaran mataimakin shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Peter Obi, wanda ya wakilci dan takaran shugaban kasa Atiku Abubakar, da tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Nuhu Ribadu wanda ya wakilci shugaban kasa Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel