Gbajabiamilla ya yi zaman farko bayan Majalisa ta 9 ta fara aiki

Gbajabiamilla ya yi zaman farko bayan Majalisa ta 9 ta fara aiki

A yau Alhamis, 6 ga Watan Yuni, 2019, majalisar ta tara (9), ta shiga bakin aiki a Najeriya. Sababbin ‘yan majalisar sun yi wani zama ne a bayan labule, wanda shi ne na karon farko.

An bude majalisar wakilan ne bayan ‘yan majalisar kasar sun aikawa shugaba Muhammadu Buhari takarda su na sanar da shi game da kafuwar majalisar kamar yadda doka ta tanada.

Sabon kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, shi ne ya jagoranci wannan zama da aka yi. Har zuwa lokacin da mu ka hada wannan rahoto, ‘yan majalisar su na tattaunawa.

Sai dai duk da wannan dogon zama da ‘yan majalisar su ka yi, rahoto ya zo mana daga jaridar Daily Trust cewa ba a nada sauran manyan mukaman da ya kamata ba ba har zuwa yau.

KU KARANTA: Tinubu ya yi magana bayan APC ta yi nasara a zaben Majalisar

Zaman da aka yi bai rasa nasaba da nadin shugaban masu rinjaye da kuma shugaban marasa rinjaye da mataimakan su, da kuma wasu manyan mukaman a majalisar wakilan tarayyar.

Haka zalika za a fitar da shugabannin wasu daga cikin kwamitocin da ya zama dole majalisa ta soma aiki da su. Daga ciki akwai kwamitin da ke kula da sha’anin yada labarai a majalisa.

A na sa rai cewa majalisar za ta dage zama har sai zuwa Ranar 2 ga Watan Yuli inda za a dumfari aiki gadan-gadan. Tuni dai Takwaran su da ke majalisar dattawa su ta tafi gajeren hutu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel