Masu neman aiki sun mamaye harabar majalisa, hoto

Masu neman aiki sun mamaye harabar majalisa, hoto

Masu neman aiki da ke fatan sabbin mambobi a majalisar wakilai su dauke su aiki sun mamaye haraba da hanyar shiga zauren majalisar yayin zamanta na ranar Alhamis.

Wasu daga cikin masu neman aikin, tsofin ma'aikata ne ga wasu mambobin majalisar da basu samu damar dawowa majalisar ba daga mazabunsu bayan kammala zaben 2019.

Masu neman aiki, wadanda yawancinsu mata ne, sun yi cirko-cirko a hanyar shiga majalisar domin samun damar mika takardunsu na neman aiki ga sabbin mambobin majalisar da zarar sun fito daga zamansu.

Masu neman aiki sun mamaye harabar majalisa, hoto

Masu neman aiki a tsaye cirko-cirko a harabar majalisa
Source: Twitter

An ga masu neman aikin na rige-rigen iskar mambobin majalisar bayan fitowarsu domin su gabatar da kansu tare da bayyana irin kwarewarsu ta aiki.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun bankado wani kamfanin kera bindigu a kudancin Najeriya

Daya daga cikin masu neman aikin ta ce tana da gogewar aiki saboda tayi aiki tare da wani mamba majalisa ta takwas da zangonta ya kare cikin makon jiya.

Matashiyar ta ce ta rasa aikinta ne saboda dan majalisar da tayi aiki tare da shi bai samu dawowa ba wannan karon.

Ta bayyana cewar tana da karfin gwuiwar cewar daya daga cikin sabbin mambobin majalisar zai dauke ta a cikin ma'aikatansa. (NAN)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel