Assha: 'Yar majalisa ta sha mari a hannun abokin aikin ta

Assha: 'Yar majalisa ta sha mari a hannun abokin aikin ta

Jami'an tsaro sun kama 'dan Majalisa mai wakiltan Wajir ta Gabas a Kenya, Rashid Amin bisa zarginsa da yi wa wata 'yar majalisa a Wajir, Fatuma Gedi duka.

The Nation ta ruwaito cewa Rashid Amin ya yi wa 'yar majalisa Fatuma Gedi duka ne a ranar Alhamis a harabar majalisar.

Rahotanni sun ce an yi ca-can baki tsakanin Gedi da Rashid kafin daga baya ya rufe ta da duka.

Dan Majalisar ya nemi sanin dalilin da ya sa Gedi da ke kwamitin kasafin kudi ta ki samar da kudaden aiki ga mazabarsa ta Wajir ta Gabas.

DUBA WANNAN: Mutane 7 da su kayi bakin jini saboda gwagwarmayar 'June 12'

Gedi ta bayyana cewa tana tare da takwarar ta mai wakiltan Homa Bay, Gladys Wanga lokacin da ta hadu da Rashid.

"Ya kira ni sakarya da sha-sha-sha sannan ya doke ni. Na razana sosai. Ban taba tsamanin hakan zai iya faruwa da ni ba. Ya kuma sake zuwa ya doke ni.

"Na fada masa cewa an bawa mazabar Wajir Ksh miliyan 100 ne kawai saboda mun kasafta kasafta kudaden zuwa yankunan da suka fi bukatar abubuwa kamar ruwa da tituna amma ya ce min hakan shirme ne," inji ta.

'Yar majalisa mai wakiltar Home Bay ta tabbatar da afkuwar lamarin inda ta ce suna hanyar su na zuwa gidan tsaro ne suka hadu da Amin.

"Sun fara magana da yaren Somali hakan ya sa na tsaya ina jiran Gedi. Mintuna kadan bayan fara maganar su sai na ga ya mari Gedi kuma ta fara kuka kuma jini na fita daga fuskantar ta. Ban san abinda ya janyo dukan ba.

"Na yi mamakin yadda dan majalisa zai yi wa takwarsa mace duka," a cewar Wanga.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta ruwaito cewa an tafi da Gedi zuwa asibiti domin bata kula.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel