Matasan Ibo sun bayar da sunan wanda suke so Buhari ya nada SGF

Matasan Ibo sun bayar da sunan wanda suke so Buhari ya nada SGF

Kungiyar matasa 'yan kabilar Ibo ta 'Ohanaeze Ndigbo Youth Council worldwide' ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sakataren gwamnatin tarayya (SGF) daga yankin kudu maso gabashin Najeriya.

A cikin jawabin da ya fitar a ranar Alhamis, shugaban kungiyar, Okechukwu Isiguzoro ya ce yin hakan zai tabbatar da adalci a rabon mukamai na kasar.

Kungiyar ta zabi tsohon ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu a matsayin wanda ta ke so a nada SGF.

DUBA WANNAN: Mutane 7 da su kayi bakin jini saboda gwagwarmayar 'June 12'

"Shugabanin Ohanaeze Ndigbo Youth council worldwide suna lura da yadda aka mayar da yankin kudu maso gabas saniyar ware wurin nadin shugabanin majalisar tarayya, fannin shari'a da hukumomin tsaro amma a maimakon suyi magiya, suna taya shugabanin majalisar murna," inji shi.

"Mu matasan Ibo mun dauki wannan a matsayin kadara daga Allah kuma muna kira da shugabanin Ibo su mayar da takubbansu su koma su fara shiri domin zaben 2023.

"Mu yi koyi da yankin Kudu maso Yamma da su kayi hakuri daga 2007 zuwa 2015 kafin suka samu ake damawa da su tare da Shugaba Buhari.

"Muna rokon ayi adalci a bawa yankin Kudu maso Gabas kujerar SGF kuma mun zabi shugaban mu da ke tsohuwar jam'iyyar ANPP, Dakta Ogbonnaya Onu a matsayin SGF mai jiran gado saboda yankin mu ta samu wakilci a majalisar zartarwa.

"Muna kyautata zaton Dakta Ogbonnaya yana da kwarewar da zai taimakawa shugaba Buhari wurin cimma burin sa na mataki na gaba. Muna kira da fadar shugaban kasa ta bawa yankin Kudu maso Gabas kujerar SGF tunda Arewa maso Gabas ce ke da Shugaban Majalisa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel