Ana wata ga wata: Dalibi dan shekarar karshe yayi yunkurin kashe kansa

Ana wata ga wata: Dalibi dan shekarar karshe yayi yunkurin kashe kansa

-Dalibin karshe a jami'ar EKSU yayi Yunkuri kashe kanshi abisa dalilin faduwa jarabawa

-Dalibin yayi kokarin kashe kansa ne ta hanyar shan wata muguwar guba

-Hukumar jam'ian ta Godewa Allah kasancewar dalibin bai mutu ba daga bisani kuma ta dorawa dalibin laifi

Wani dalibi dan shekarar karshe a jami’ar jihar Ekiti (EKSU) wanda aka fi sani da kwamared Zamane yayi yunkurin kashe kansa sanadiyyar faduwa jarabawa.

Wata majiya ta ce ya sha wata muguwar guba ne, haka kuma wasu na tunanin dalibin ya yanki kanshi ne da wani abu mai kaifi wanda a halin yanzu yana a asibitin koyarwa na jami’ar ta Ekiti.

Akindeko, dalibin karshe na kulliyar koyan aikin banki ya dade yana daukin fitowar sakamokan jarabawarsa. Amma da sakamakon ya fito sai yaga ya fadi darasi daya tak wanda hakan ya sanya sai ya kara shekara guda.

Kafin yayi yunkurin kashe kansa, Akindeko ya tura wasu sakonni a wani dandalin sada zumunta na whatsapp wanda ya nuna rashin jin dadinsa da kuma fidda kauna daga karatu darayuwa baki daya.

Ya rubuta kamar haka “duk abinda ya faru yau baiyi dadi ba, Allah ka taimake ni kada ka saka ni bakin ciki”

Ya kara da cewa “ Me ya sanya yau ta zo a haka, Allah ka taimaka mani wannan watan. Tun farkon wannan watan komi ya daburce mani.”

“Abinda kawai nike bukata yanzu shine in aikata laifin da za ayi mani daurin rai da rai. Saboda haka kowa yayi hattara kada laifin ya afka mashi”

Bana bukatar ilimi da rayuwa yanzu. Ina tunanin lokaci yayi da zan tafi. Na rubuta wannan ne saboda ko da kun kirani ko kun turo mani sako ta waya ban amsa maku ba. Allah ya taimaki wa yanda suke raye”

“ Nayi da na sanin zuwa wannan duniyar, nayi da na sanin neman ilimi, na rantse EKSU tsinannan makaranta ce”

KARANTA WANNAN: Allah Ya tona asirin Limamin da ya shirya damfarar mabiyansa N3,000,000

Wani abokin Akindeko dake jinyarshi mai suna Mayowa yace yanzu Akindeko na cikin hayyacinsa.

Hukumar makarantar ta EKSU ta tabbatar da afkuwar lamarin. Haka zalika ta dora laifi ga Akindeko da yayi kokarin kashe kasnhi mai makon ya shiga ajin da ake gabatarwa lokacin hutu don dalibai masu gyara su gama da wuri.

“Don me mutum zaiyi kokarin shan guba? Rayuwa cike take da kalubale. Wa yace bazaka sake faduwa ba ? kasan mutum nawa suka gaza a duniyar nan? Kasan ko sau nawa Abraham Lincoln (Tsohon shugaban kasar Amurika) yayi takara ya rasa?”

“Mun gode ma Allah bamu rasa shi ba, ya samu sauki yanzu kuma yana cikin hayyacinshi a asibiti. Amma hakan baya nufin jami’ar na da tsanani ko mugunta ga dalibai. Yana a asibitin koyarwa na jam’ar EKSU kuma ya samu sauki yanzu” inji jam’in hulda da jama’a na jami’ar.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar

jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel