DSS: An damke wadanda ke zanga-zanga a cikin Garin Ibadan

DSS: An damke wadanda ke zanga-zanga a cikin Garin Ibadan

Dakarun hukumar DSS na kasa sun cafke wasu mutane da aka kama su na zanga-zanga a Garin Ibadan da ke jihar Oyo. Kafin nan jami’an tsaron sun dakatar da wannan zanga-zanga da ake shirya.

Kamar yadda mu ka samu labari a Ranar 12 ga Watan Yuni, 2019, jami’an na DSS masu fararen kaya su ka tsaida wani zanga-zanga da wasu gungun Yarbawa su ka shirya a babban birnin jihar Oyo.

An shirya gangamin ne a lokacin da ake tunawa da bikin damukaradiyya a kasar da kuma makokin Marigayi MKO Abiola wanda ya rasu shekaru da-dama da su ka wuce a cikin gidan yari.

Kamar yadda mu ka samu labari, daga cikin wadanda jami’an tsaron su ka kama akwai shugaban wata kungiyar kasar Yarbawa mai suna “Oodua Coalition Against Insurgency”, Tunde Hamzat.

Dr. Tunde Hamzat ya saba sa-baki wajen harkokin yau da kullum a yankin jihar Oyo da kewaye. Sannan kuma akwai wata Baiwar Allah mai suna Princess Oyeronke da yanzu ta na tsare.

KU KARANTA: Batutuwan da Buhari ya yi magana a kai a Ranar bikin Damukaradiyya

Jami’an na DSS sun yi maza sun dakatar da zanga-zangar da aka fara ne da kimanin karfe 7:00 na safe a gaban gidan gwamnatin jihar Oyo, sannan su ka yi ram da jagorori 3 na wannan tafiya.

Yanzu dai wadannan mutane da aka kama su na Hedikatar DSS na jihar da ke cikin Garin Aleshinloye. Wani shugaban kungiyar OPC a jihar ya tabbatar da wannan labari a Ranar Laraba.

Adesina Akinpelu ya bayyanawa manema labarai akasin rahoton da a ka ji, inda ya ce sun samu lasisin shirya wannan zanga-zanga, amma kwatsam su ka ji jami'an DSS sun zo sun kama jama'a.

Akinpelu ya bayyana cewa sun shirya wannan zanga-zanga ne domin su koka da halin rashin tsaro da ake ciki a kasar Yarbawa na sace jama’a da garkuwa da su, da kuma hare-hare a gonaki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel