HDP ta roki kotun zabe da ta soke zaben Shugaban kasa

HDP ta roki kotun zabe da ta soke zaben Shugaban kasa

Jam’iyyar Hope Democratic Party (HDP) da dan takararta na shugaban kasa, Albert Oworu, a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni, sun roki kotun zaben Shugaban kasa da ta soke zaben shugaban kasar da aka gudanar a 23 ga watan Fabrairu.

Oworu da yake bayani ya bayyana zaben a matsayin “raba gardama” kawa amma ba wai zabe ba.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa a cikin rubutacciyar kararta mai lamba CA/ PEPC/001/2019, jam’iyyar ta bukaci kwamitin da ta soke sakamakon zaben tare da bada umurnin gudanar da sabon zabe.

Owuru wanda ya samu kuri’u 1,663 a zaben shugaban kasa ya dage cewa zaben da aka gudanar ya saba ma dokar zabe.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Jam’iyar PDP da Atiku Abubakar a ranar Alhamis sun roki kotun sauraren korafe-korafen zabe da ta basu damar binciken shafin yanar gizo na hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.

KU KARANTA KUMA: Majalisar Kaduna: Dan takarar gwamnati mai shekaru 39 ya lashe zaben kakakin majalisa

Har ila yau, jam’iyar ta PDP ta sake rokon kotun sauraren korafe-korafen zabe da ta basu damar binciken na’urorin zamani wadanda akayi aiki dasu a zaben 23 ga watan Faburairu na shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel