INEC zata hada kai da Majalisar dokoki ta domin yi wa tsarin zabe garanbawul

INEC zata hada kai da Majalisar dokoki ta domin yi wa tsarin zabe garanbawul

-INEC na cigaba da bitar yadda zaben 2019 ya wakana, inda shugaban hukumar ya bayyana cewa zasu kammala bitar cikin watanni biyu ne kacal.

-Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta yace kungiyarsu a shirye take wurin hada hannu da sabuwar majalisar dokoki domin yi wa kundin tsarin gudanar da zabe kwaskwarima gabanin zabe mai zuwa.

Gabanin zabukan dake tafe nan gaba a Najeriya, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana aniyar da take dashi na yin garanbawul ga kundin dokokin zaben kasar nan.

Hukumar ta bayyana cewa zata tuntubi majalisar dokoki ta 9 kan yadda za’a sake habbaka tsarin gudanar da zabukan kasar nan.

KU KARANTA:Atiku da PDP sun roki kotu wata alfarma guda daya

Hukumar INEC na cigaba da gudanar da taron bitar zaben 2019, inda ta bada tabbacin cewa zata kammala bitar cikin watanni biyu masu zuwa.

Har ila yau, hukumar ta bayyana cewa dukkanin ababen da aka tattauna yayin bitar za’ayi amfani dasu domin yin kwaskwarima ga kundin tsarin dokokin zaben Najeriya.

Shugaban hukumar zaben mai zaman kanta, Farfesa Mahmood Yakubu shi ne ya bada wannan sanarwa yayin da ya karbi bakwancin tawagar Majalisar dinkin duniya, wacce Sahel Muhammad ya jagoranta a ofishinsa dake Abuja ranar Alhamis.

Shugaban ya ce: “ Kofofinmu na sauraron shawarwari a bude suke domin inganta tsarin zaben Najeriya saboda zabukan dake tafe nan gaba. Abu na farko da zamu karkata hankalinmu a kai shi ne yiwa kundin tsarin zaben garambawul.”

Mahmood ya cigaba da cewa: “ Mun dade muna da kundirin yin haka tun kafin zaben 2019, amma hakan bai yiwu ba saboda kurewar lokaci. Mun fara wannan aikin ne tare da majalisa ta 8 bisa la’akari da matsolin da aka fuskanta a zaben shekara ta 2015.”

“ Ina mai bada tabbaci ga al’ummar Najeriya cewa, tabbas za muyi gyara ga tsarin gudanar da zabe a kasar nan gabanin zaben da za’ayi nag aba. Hakan kuwa zai kasance ne kawai ta hanyar hada hannu da sabuwar majalisar dokoki ta 9.” A cewar shugaban INEC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel