Shugaba Buhari ya bayyana rukunin mutane 2 da ba su son ganin Najeriya ta zauna lafiya

Shugaba Buhari ya bayyana rukunin mutane 2 da ba su son ganin Najeriya ta zauna lafiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shuwagabannin addinai da shuwagabannin siyasa, ma’ana Malamai da yan siyasa ne ke rura duk wutar duk wani rikici a Najeriya, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaba Buhari ya bayyana haka ne sa’ilin da yake gabatar da jawabinsa yayin bikin ranar dimukradiyyar Najeriya daya gudana a dandalin Eagle Square dake babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni.

KU KARANTA: Bagudu ya ki tabbatar dani a matsayin Alkalin Alkalai saboda ni kirista ce, inji Alkalin Alkalai

A cewar Buhari, duk matsalolin tsaron da Najeriya ke fama da ita a yanzu ya samo asali ne daga wajen shuwagabannin addinai da kuma manyan yan siyasa domin biyan buktarsu tare da kokarin gurgunta kasar gaba daya.

“Yawancin rikicin da ake fama dashi tsakanin jama’a ko rikicin addini suna samo asali ne daga wajen yan siyasa dake daukan nauyin hare haren, ko kuma malaman addinai da suke tunzura mabiyansu, ko kuma shuwagabannin kabilu dake umartar yan kabilarsu su kashe wasu, da haka suke gurgunta kasarmu Najeriya.” Inji shi.

Da wannan ne shugaban kasa Buhari ya dauki alkawarin tabbatar da Najeriya ta zauna a matsayin kasa daya al’umma daya, tsintsiya madaurinki guda, yan kasa su zauna cikin hadin kai ba tare da nuna bambamci ko wariya ga wani ba.

“Dani aka yi gwagwarmayar tabbatar da Najeriya kasa daya al’umma daya, don haka zan sadaukar da sauran abinda ya rage min a rayuwata domin ganin Najeriya ta zauna cikin hadin kai da kuma inganta rayuwar yan Najeriya.” Inji Buhari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel