Baka cancanci mulkin Kaduna ba - Shehu Sani ya yiwa El-Rufai kaca-kaca

Baka cancanci mulkin Kaduna ba - Shehu Sani ya yiwa El-Rufai kaca-kaca

- Tsohon Sanata Shehu Sani ya caccaki Gwamna El-Rufai, inda ya kira shi da mai muguwar manufa

- Ya ce babu abinda ya iya idan ba ya dinga amfani da shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cika burinsa ba

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya kira gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai da mutum mai muguwar manufa, inda ya bayyana cewa duk da kokarin da ya dinga yi na yaga ya samu ya zama shugaban gwamnonin Najeriya amma hakan bai yiwu ba.

Ya kara da cewa gwamnan bai cancanta ya mulki jihar Kaduna ba.

Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar, yayin da yake mayarwa da gwamnan martani akan maganar da yayi ta cewa ya yiwa Sanatan da shi da takwaransa Sanata Suleiman Hunkuyi murabus a siyasa.

A martanin na sa, Shehu Sani ya bayyanawa gwamnan cewa bai isa ya ce ya yiwa wani murabus a siyasa ba, tunda shi babu abinda ya iya a rayuwarsa, sai dai yaje ya dinga amfani da shugaban kasa Muhammadu Buhari wurin cimma burikansa.

KU KARANTA: Shehu Sani: Sai da 'Yar Adua ya bawa Abiola shawara akan ya dauki Atiku a matsayin mataimakinsa yaki yarda

Sanatan ya ce: "Hankali na yazo kan wata magana da Nasir El-Rufai yayi, inda ya kira sunana dana Sanata Suleiman Hunkuyi. Duk da cewa har yanzu kotu na sauraron karar dana kai gwamnan a shekarar data gabata, amma duk da haka ya kamata nayi magana akan abinda gwamnan yace.

"Baka isa ka yi ikirarin cewa kayi wa wani murabus ba, bayan babu abinda ka iya a rayuwarka idan ba makalewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kana cimma wasu burika naka ba.

"Har yanzu baka cika mai cikakken iko ba, tunda ka kasa lashe zaben shugaban gwamnonin Najeriya wanda aka yi kwanakin baya."

Ya kara da cewa: "Kowa ya sani a Najeriya, kuma nayi imani cewa lokaci kadan ya rage kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gano bakin halayenka, idan har ya kai lokacin da bashi da amfani a gareka.

"Ba kai ne mutum na farko da ya fara lashe zabe ba a Kaduna, dan haka kuma baza ka zama na karshe ba, ko Makarfi da yayi shekara takwas yana mulki bai cika bakin cewa ya yiwa mutane murabus ba. Kuma su lokacin da suka ci zabe babu wanda yayi zargin cewa sun aikata magudi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel