Majalisar dattawa ta dage zamanta zuwa 2 ga watan Yuli, ta kafa kwamitin mutum 12 na wucin-gadi

Majalisar dattawa ta dage zamanta zuwa 2 ga watan Yuli, ta kafa kwamitin mutum 12 na wucin-gadi

Majalisar dattawa a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni ta dage zamanta zuwa ranar Talata, 2 ga watan Yuli don bada damar yin rabe-raben kujeru da ofisoshi ga sanatoci.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ovie Omo-Agege ne ya gabatar da wannan batun sannan Sanata Philip Aduda ya mara masa baya bayan an share awa daya ana ganawa.

A halin da ake ciki, majalisar dattawa ta kafa kwamitin wuci-gadi na mutum 12 karkashin jagorancin Sanata Abu Kyari, wanda aka daura wa alhakkin hada kai da ma’aikatar majalisar don jin dadin Sanatocin.

An ba kwamitin, wanda ke kunshe da mambobi daga yankuna shida kamar yanda shugaban majilisa Ahmad Lawan ya bada sanarwa, mako biyu domin su gabatar da rahotonsu sannan za su yi aiki tare da magatakardar majalisa, Nelson Ayewoh, wajen ganin an tabbatar da rabe raben kujeru da ofisoshi ga dukkan sanatocin a dan lokacin da aka bayar.

KU KARANTA KUMA: Majalisar Kaduna: Dan takarar gwamnati mai shekaru 39 ya lashe zaben kakakin majalisa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sabon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya rantsar da tsohon gwamnan jihar Imo, Owelle Rochas Okorocha a matsayin Sanata mai wakiltan Imo ta yamma a majalisar dokokin tarayya, a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni.

Magatakardar majalisar dattawa, Nelson Ayewoh, ne ya gudanar da taron rantsarwar bayan Okorocha ya sanya hannu a takardun da ya kamata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel