Atiku da PDP sun roki kotu wata alfarma guda daya

Atiku da PDP sun roki kotu wata alfarma guda daya

-Atiku da jam'iyarsa ta PDP na neman izinin kotun sauraren korafe-korafen zabe domin binciken kayayyakin da hukumar zabe mai zaman kanta tayi aiki dasu a zaben 23 ga watan Faburairun 2019.

-Jam'iyar ta PDP na cigaba da ikirarin cewa ita ce tayi nasara a zaben shugaban kasan da ya gabata ba APC ba.

Jam’iyar PDP da Atiku Abubakar a ranar Alhamis sun roki kotun sauraren korafe-korafen zabe da ta basu damar binciken shafin yanar gizo na hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.

Har ila yau, jam’iyar ta PDP ta sake rokon kotun sauraren korafe-korafen zabe da ta basu damar binciken na’urorin zamani wadanda akayi aiki dasu a zaben 23 ga watan Faburairu na shugaban kasa.

KU KARANTA:Rashin tsaro: Gwamnan Zamfara ya gana da kungiyar Miyetti Allah

Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa, cikin korafin da Atiku shi da jam’iyar PDP suka shigar gaban kotun ya hada da, ikirarin cewa jam’iyarsu ce ta lashe zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Faburairun 2019, bisa sakamakon da su kace yana nan kunshe a shafin yanar gizon INEC.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta karyata wannan magana da jam’iyar PDP tayi game da sakamakon zaben ranar 23 ga watan Faburairun 2019 wanda ta yi ikirarin cewa ta samo daga shafin hukumar na yanar gizo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel