Hajjin 2019: Kaduna ta sanya 20 Yuni a matsayin ranar karshe ta biyan kudin aikin

Hajjin 2019: Kaduna ta sanya 20 Yuni a matsayin ranar karshe ta biyan kudin aikin

-Hukumar jin dadin alhazai ta Kaduna ta sanya ranar Alhamis 20 ga Yuni 2019 a matsayin ranar karshe ta biyan kudin aikin hajjin bana daga maniyyata.

-Dole mu rufe karbar kudin hajjin a ranar 20 ga watan Yuni don cimma ranar da Hukumar ta kasa ta kayyaje- Jami'in hulda da jama'a na Hukumar Alhazai ta Kaduna

Jami’in hulda da jama’a na hukumar jin dadin alhazan ta Kaduna Yunusa M. Abdullahi, ya fitar da jawabi inda ya bayyana cewa dole ya zama a sanya ranar karshe don a cimma ranar da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta kasa ta sanya na 21 ga watan Yuni 2019.

KARANTA WANNAN: Majalisar Kaduna: Dan takarar gwamnati mai shekaru 39 ya lashe zaben kakakin majalisa

Bayanin yayi gargadi cewa duk wanda bai cika kudinsa ba to zai rasa samun damar tafiya aikin hajjin kasancewar Hukumar ta kasa ta kayyaje 21 ga watan Yuni a matsayin rana ta karshe da kowane maniyyaci zai cika kudinsa

Hukumar hajjin ta yanke kudi Naira 1,549,297.09 a matsayin kudin aikin hajjin bana. maniyyata aikin hajji da suka bayar da ajiyar kudinsu zasu cika sauran kudaden ko kuma su rasa gurbin da aka ajiye masu.

A wani labari mai kama da wannan, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Sokoto, ta bayyana 15 ga watan Yuni a matsayin ranar karshe da dukkan maniyyata aikin hajji na jihar zasu cika kudinsu na aikin hajjin.

Haka zalika, babban daraktan hukumar, Muhammadu Dange ya bayyana cewa hukumar ta kayyaje kudi Naira 1,540,428.10 a matsayin kudin aikin hajjin wannan shekarar.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel