Yanzu Yanzu: Sanatocin APC sun ki yarda ayi muhawara kan jawabin Buhari na ranar Damokradiyya

Yanzu Yanzu: Sanatocin APC sun ki yarda ayi muhawara kan jawabin Buhari na ranar Damokradiyya

Sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki sun dakile batun da ke neman majalisar dattawa tayi muhawara akan Jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a ranar 12 ga watan Yuli, a bikin ranar Damokradiyyar Najeriya.

Sanata Istifanus Dung Gyang (PDP,Plateau) ne ya gabatar da batun a zauren majalisar dattawa.

Ya bukaci abokan aikinsa a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni da su amince a tattauana batun a matsayin abu mai muhimmanci a kasar.

Yace: “Batun yana da alaka da jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a ranar Damokardiyya. Jawabin ya yadu kuma ya janyo cece kuce da dama.”

A lokacin da shugaban majalisa Ahmed Lawan ya baiwa yan majalisan damar zabe da kafa matsaya akan batun, yawancin sanatocin, wadanda akasarinsu yan APC ne sun ki amincewa da hakan.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisar dattawa: Ndume ya sake magana akan kayen da ya sha a hannun Lawan

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Ahmad Lawan a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni ya gudanar da aiki na farko a matsayin sabon Shugaban majalisar dattawan Najeriya, inda ya rantsar da Sanata Rochas Okorocha a matsayin mai wakiltan yankin Imo ta yamma a majalisar.

Taron ya gudana ne jim kadan bayan majalisar dattawa ta gabatar da addu’o’i, da sauransu a zauren majalisar da ke Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel