Shehu Sani ya yabawa Buhari amma ya nemi a gyara babban filin wasan da ke Abuja

Shehu Sani ya yabawa Buhari amma ya nemi a gyara babban filin wasan da ke Abuja

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya tofa albarkacin bakinsa bayan da ya samu labari cewa an canzawa babban filin wasan Najeriya da ke Garin Abuja suna.

A Ranar 12, ga Watan Yuni, 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canzawa filin wasannin Najeriya da ke cikin Garin Abuja suna domin a rika tunawa da Marigayi Alhaji Mashood Abiola.

Shehu Sani, wanda ya na cikin wadanda su ka wakilci yankin jihar Kaduna a majalisa ta takwas, ya nuna goyon bayansa ga wannan mataki da shugaban kasar ya dauka a tsakiyar makon nan.

Sanatan ya fito shafin sa na Facebook da Tuwita ya na magana a kan wannan batu, inda ya ce shugaban kasa Buhari ya yi abin a-yaba. Shehu Sani ya yi wannan bayani ne a Ranar Larabar nan.

KU KARANTA: Batutuwan da Buhari ya yi magana a kai a Ranar bikin Damukaradiyya

Tsohon ‘dan majalisar ya ce Mashood Kashimawo Abiola ya cancanci a sa sunansa a filin wasan da Najeriya ta ke ji da shi, domin kuwa ya kasance yana sha’awar wasanni a lokacin ya na raye.

Sai dai tsohon Sanatan ya ce ba sanyawa filin wasan sunan Marigayi Abiola ne kurum abin da za ayi ba, ya nemi gwamnatin kasar ta gyara wannan fili wasa, wanda ya ce ya dade da sukurkucewa.

Daga baya Shehu Sani ya bada labarin abin da Marigayi Shehu Yaradua ya fada masa a game da zaben shugaban kasar da aka yi na 1993, inda yace an so ne Abiola ya tafi da Alhaji Atiku Abubakar.

A daidai lokacin da ake bikin tunawa da wannan rana a Najeriya, an ga Sanatan a gaban Gidan MKO Abiola. Marigayi MKO Abiola yana kan lashe zaben shekarar 1993 ne, sai kwatsam a ka soke zaben.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel