Shehu Sani: Sai da 'Yar Adua ya bawa Abiola shawara akan ya dauki Atiku a matsayin mataimakinsa yaki yarda

Shehu Sani: Sai da 'Yar Adua ya bawa Abiola shawara akan ya dauki Atiku a matsayin mataimakinsa yaki yarda

- Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana wata shawara da 'Yar Adua ya bai wa Abiola akan Atiku Abubakar

- 'Yar Adua ya bai wa Abiola shawara akan ya zabi Atiku Abubakar a matsayin mataimakin shugaban kasa yaki yarda da shawararsa

Tsohon Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bayyana yadda wata hirarsu ta kasance da marigayi Shehu Musa Yar'adua a lokacin da suka hadu a gidan yari.

Shehu Sani ya ce, 'Yar Adua ya fada min cewa sai da ya bai wa Abiola shawara akan ya dauki Atiku Abubakar a matsayin mataimakinsa a lokacin da ya fito takarar shugaban kasa, amma sai Abiola ya ki yarda da shawararsa, ya dauki Babagana Kingibe a matsayin mataimakinsa a zaben da aka yi ranar 12 ga watan Yuni 1993.

MKO Abiola da Babagana Kingibe ne dai ake tunanin sun lashe zaben shugaban kasa a shekarar 1993, duk da dai cewa ba a bayyana sakamakon zaben ba.

KU KARANTA: Tirkashi: Wasu mata sun sace jaririya daga zuwa barka a Zariya

Bayan dawowar mulkin farar hula lokacin Obasanjo, sai ya dauki Atiku Abubakar a matsayin mataimakinsa na shugabancin kasa, hakan yasa suka ci zabe har sau biyu a tare a shekarar 1999 da kuma shekarar 2003.

Sanata Shehu Sani ya wallafa wannan rubutun nasa a shafukansa na Facebook da Twitter, ya kuma yi bayani kamar haka: "A lokacin da muke tsare a gidan yarin Kirikiri a shekarar 1995, Marigayi Shehu Musa 'Yar Adua ya bayyana min cewa sai da ya shawarci MKO Abiola da ya dauki Alhaji Atiku Abubkar a matsayin mataimakin shugaban kasa, amma sai yaki yarda da shawara ta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel