Ahmad Lawan ya aiwatar da aikin farko a matsayin Shugaban majalisar dattawa

Ahmad Lawan ya aiwatar da aikin farko a matsayin Shugaban majalisar dattawa

- Sabon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya aiwatar da aiki na farko a matsayin jagorar majalisar

- Ya rantsar da Sanata Rochas Okorocha a matsayin mai wakiltan yankin Imo ta yamma a majalisar

Sanata Ahmad Lawan a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni ya gudanar da aiki na farko a matsayin sabon Shugaban majalisar dattawan Najeriya, inda ya rantsar da Sanata Rochas Okorocha a matsayin mai wakiltan yankin Imo ta yamma a majalisar.

Taron ya gudana ne jim kadan bayan majalisar dattawa ta gabatar da addu’o’i, da sauransu a zauren majalisar da ke Abuja.

Lawan ya rantsar da Okorocha a zauren majalisar da misalin karfe 10:39 na safe.

Legit.ng ta ruwaito cewa a ranar Talata, 11 ga watan Yuni ne yan majalisar suka zabi Lawan da Sanata Ovie Omo-Agege a matsayin Shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa.

KU KARANTA KUMA: Kafin ka fitar da yan Najeriya daga kangin talauci, ka fara fitar dasu daga kangin yan bindiga – Shehu Sani

A baya mun ji cewa Sanatan Borno, Ali Ndume, a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni yace ya ajiye lamarin kaye da ya sha a hannun Ahmed Lawan wajen neman kujerar shugabancin majalisa a kefe.

Mista Ndume yayi takara da sabon Shugaban majalisar dattawa, Mista Lawan, a lokacin rantsar da majalisar dattawa ta tara wanda aka gudanar a ranar Talata, 11 ga watan Yuni.

Da yaki jin duk wani rarrashi da aka yi masa domin ya janye, Mista Ndume yace lallai sai yayi takarar wannan kujera.

Sai dai ya sha kaye a hannun Lawan bayan anyi zaben inda ya samu kuri’u 28.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel