Jagoran APC Tinubu ya aikawa sababbin shugabannin majalisa sakon murna

Jagoran APC Tinubu ya aikawa sababbin shugabannin majalisa sakon murna

Babban Jigon jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fito ya yi magana bayan kammala zaben majalisar wakilai da kuma dattawan da aka yi a cikin makon nan.

Bola Tinubu ya yi magana ne a Ranar Laraba, 12 ga Watan Yuni, 2019, inda ya taya wadanda su ka lashe zaben murna, sannan kuma ya yi kira da ‘yan majalisar su hada kai da shugaban kasa.

Tinubu ya bayyana wannan ne a wani sako da ya aikowa sababbin shugabannin da za su rike majalisar tarayyar. Jigon na APC ya aika wannan sako ne ta bakin Hadiminsa, Tunde Rahman.

A jawabin da Rahman ya fitar, Tinubu ya fito ya na cewa:

“Ina taya Ahmad Lawan Femi Gbajabiamila da mataimakan su; Ovie Omo-Agege Alhaji Ahmed Idris Wase, murnar zama shugabannin majalisa ta tara. Wannan gagarumar nasara da su ka samu ya nuna irin yadda aka yarda da su”

KU KARANTA: Tsohon Sanatan najeriya ya maidawa Buhari martani

Tinubu ya cigaba da cewa:

“Ya kamata majalisar tarayya ta dawo daga rakiyar zaman gaban da aka rika yi a baya, ta shirya kulla kawance da bangaren masu zartarwa. Hadin-kai tsakanin majalisa da shugaban kasa, shi ne zai kai kasar ga cin da ake buri.”

Jawabin na jagoran na APC ya ce:

“Tsarin kasar mu yana son taimakekeniya tsakanin masu iko da majalisa, kuma bai hana a yi aiki tare da juna cikin jituwa ba domin a taimaki al’umma.”

Tinubu ya kara da cewa wannan nasara da ‘yan majalisar su ka samu ya zo daidai da lokacin da Najeriya ta cika shekaru 20 ta na kan tsarin mulkin farar hula, don haka ya tuna da tsofaffin gwarazan kasar.

Asiwaju Bola Tinubu ya kare jawabin na sa da yabawa wadanda su ka nemi takara, amma su ka sha kashi, ya kuma yi kira gare su da su ajiye duk wani banbanci, su yi aiki da tare da junansu.

“Ina wa shugaban majalisar dattawa da na wakilai da kuma mataimakansu da duk ‘yan majalisar kasar fatan alheri, su cika wa’adin su lafiya.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel