Kafin ka fitar da yan Najeriya daga kangin talauci, ka fara fitar dasu daga kangin yan bindiga – Shehu Sani

Kafin ka fitar da yan Najeriya daga kangin talauci, ka fara fitar dasu daga kangin yan bindiga – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani yayi martani ga jawabin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari game da fitar da yan Najeriya miliyan 100 daga talauci cikin shekaru 10.

Sanatan a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni ya bayyana cewa mutane na bukatar a fitar dasu daga kangin ta’addanci kafin a fitar dasu daga kangin talauci.

Hakazalika Sani ya bayyana cewa mutane na bukatar a ceto su daga lamarin ta’addanci inda ya lissafa su a matsayin matsalar makiyaya, masu garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe.

Sanata Sani yace mutane na iya nema wa kansu mafita daga talauci idan aka basu damar da za su iya fita gonakinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoron hare-hare ba.

Ga yadda sanatan ya wallafa a shafinsa na twitter: “Kafin ka fitar dasu daga kangin talauci ka fara fitar dasu daga kangin yan bindiga

“A yanzu mutanenmu kawai na so a fitar dasu daga kangin ta’addanci, makiyaya, masu garkuwa da mutane da kashe-kashe; da kansu za su dauki matakin fita daga talauci, da zaran sun fara samun ikon fita aiki a gonakinsu cikin kwanciyar hankali.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Lawan ya rantsar da Okorocha a matsayin Sanata

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin fitar da yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci zuwa ga tafarkin ci gaba a shekaru 10 masu zuwa.

Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin bude taro a wajen bikin ranar 12 ga watan Yuni, wacce ta kasance ranar bikin Damokradiyya a Abuja.

Shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da bunkasa tattalin arziki domin fitar da Najeriya daga talauci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel