El-Rufai ya yiwa Shehu Sani da Hunkuyi fatan yin ritaya mafi cancanta

El-Rufai ya yiwa Shehu Sani da Hunkuyi fatan yin ritaya mafi cancanta

Gwamna Nasir El-rufai na jihar Kaduna ya yiwa tsoffin sanatocin jihar Kaduna, Hunkuyi da Shehu Sani fatan yin ritaya mafi cancanta.

Gwamnan ya fadi hakan ne a shafinsa na Facebook a ranar 11 ga watan Yuni yayinda yake taya sabbin sanatocin Kaduna, Suleiman Abdu Kwari da Uba Sani murna.

Da yake ci gaba da jawabi, gwamnan ya kaddamar da cewa biyayyarsa da aminci gaa abokan arziki na din-din-din ne yayinda adawa da kuma kiyayya ga maciya amana ya kasance na din-din-din.

Karanta rubutun:

Babu batacciyar soyayya a tsakanin Sani da El-Rufai. A lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Kaduna, Sani ya fadi a wajen samun tikitin jam’iyyar inda hadimin Gwamna El-Rufai kan harkokin siyasa, Malam Uba Sani yayi nasara.

Kwamitin jam’iyyar na kasa a baya ta bada tikiti kai tsaye ga Sani wanda El-Rufai, wasu yan takara da sauran shuwagabannin jam’iyyar suka yi zanga zangan rashin amincewa da haka.

A cewar rahoton, gwamnan ya nuna rashin amincewa da tikitin sanatan a majalisan.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisar dattawa: Ndume ya sake magana akan kayen da ya sha a hannun Lawan

Sakamakon rashin nasaransa, Sani ya bar APC ya koma jam’iyyar People’s Redemption Party (PRP) a ranar 3 ga watan Oktoba, kwana uku bayan barinsa All Progressives Congress (APC). Sani ya bayyana hakan ne a wani jawabin da hadiminsa Mista Suleiman Ahmed ya gabatar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel