Yanzu Yanzu: Lawan ya rantsar da Okorocha a matsayin Sanata

Yanzu Yanzu: Lawan ya rantsar da Okorocha a matsayin Sanata

Sabon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya rantsar da tsohon gwamnan jihar Imo, Owelle Rochas Okorocha a matsayin Sanata mai wakiltan Imo ta yamma a majalisar dokokin tarayya, a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni.

Magatakardar majalisar dattawa, Nelson Ayewoh, ne ya gudanar da taron rantsarwar bayan Okorocha ya sanya hannu a takardun da ya kamata.

Da farko an janye takardar shaidar cin zabe na tsohon gwamnan bayan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tace jami’inta ya sanar da sakamakon zaben ne a karkashin matsin lamba bayan zaben sanata wanda aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

A ranar rantsar da majalisar dattawa ta tara, Mista Okorocha ya halarci wajen taron da safe amma ba a rantsar dashi ba bayan hukumar majalisar sun ki tantance shi.

Hukumar INEC ta dai ki bashi takardar shaidar cin zabe duk da cewar wata kotun tarayya ta umurce ta da ta aikata hakan.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisar dattawa: Ndume ya sake magana akan kayen da ya sha a hannun Lawan

Sai dai kuma daga bisani a ranar Talata, INEC ta yanke shawarar baa Okorocha takardar cin zaben nasa, amma bisa cewa za ta daukaka kara akan hukuncin kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel