An shiga rudani bayan likitar bogi ta sace jaririya yar kwana 3 daga asibitin Plateau

An shiga rudani bayan likitar bogi ta sace jaririya yar kwana 3 daga asibitin Plateau

- An sace jaririya daga asibitin kwararru na jihar Plateau, kwanaki uku bayan haihuwarta

- An tattaro cewa wata mata da tayi ikirarin kasance likita a asibitin c eta sace jaririyar

- Uwar dan tace likitar bogin tace likita ya fada mata cewa jinjirarta na bukatar kammala wasu gwaje-gwaje

An kaddamar da batar wata jaririya sabuwar haihuwa daga asibitin kwararru na jihar Plateau, Jos, inda har yanzu mahaifiyarta ke kwance.

An haifi jaririyar mallakar Nwa God Chukwuebuka, 33 da Mary Chukwuebuka, 30, a ranar 28 ga watan Mayu sannan wata mata da ta badda kama a matsayin likitar asibitin ta sace ta a ranar 31 ga watan Mayu.

Da suke Magana da manema laarai, iyayen jinjirar sunce an haifi yarinyar a safiyar ranar 28 ga watan Mayu bayan an sa wa mahaifiyarta abun haihuwa.

Daily Trust ta ruwaito cewa Mary tace ta ci gaba da kasance a asibitin saboda ta zubar da jini sosai a lokacin haihuwa.

Mahaifiyar jinjirar tace: “Da yammacin ranar Alhamis, likitan ya bani fam din yin gwaji sannan washegari da safe, wata mata sanye da kayan likita tazo ta tambaye ni fam din.

“Sai na bata takardar, amma tace ba wannan ba, fam din gwaji na jinjirar. Na fada mata cewa likita bai ce wani abu na damun jaririyata ba, amma tace akwai gwajin jini da ya kamata ayi kuma kasancewarta likita sai na aminta da iya sannan na mika mata yarinyar,” inji Mary.

Ta kuma bayyana cewa mahaifiyarta wato kakaar yarinyar ta bi likitar ta bogi zuwa dakin gwaji amma aka nemi ta tafi cewa likitar tayi alkawarin dawo da jinjirar da zaran an gama gwajin jinin.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisar dattawa: Ndume ya sake magana akan kayen da ya sha a hannun Lawan

Da yake tabbatar da lamarin, Shugaban likitocin asibitin, Dr Philimon Golwa, yace lamarin baya rasa nasaba da wata mata da ta ziyarci asibitin kafin bacewar jaririyar.

Golwa yace matar tayi ikirarin cewa tana da ciki amma gwajin likitoci ya nuna cewa cikin karya ne.

Likitan yace matar ta zo asibitin ne da wani mutumi da tayi ikirarin mijinta ne inda suka haddasa rigima.

“Bayan faruwar lamarin, malaman jinya sun shawarci marasa lafiya da su kula da yaransu sannan su je garesu idan akwai wani abu kawai sai muka ji cewa wata mata sanye da kayan likitoci ta karbi wata jinjira daga wajen mahaifiyarta sannan uwar yarinyar bata kai kara ba sai bayan kusan awa guda,” inji Golwa.

Ya kuma tabbatar da cewa sun sanar da yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel