Kuma dai: Wani dalibi ya hallaka kansa a jihar Kebbi

Kuma dai: Wani dalibi ya hallaka kansa a jihar Kebbi

Wani dalibin kwalejin Waziri Umaru Polytechnic da ke Birnin Kebbi mai suna Solomon Benedict, ya hallaka kansa saboda rashin kudi da talauci.

Rahotanni sun nuna cewa Solomon Benedict ya kashe kansa ne ta hanyar shan maganin kwari hade da madarar yogut.

Daya daga cikin abokansa wanda yayi hira da jaridar Daily Trust ya ce "Mun lura cewa ba cikin lafiya. Ya rike cikinsa sannan muka gano cewa za zuba maganin kwari cikin abin shan."

Marigayi Benedict ya dade yana barazanar cewar zai hallaka kansa sau tari saboda talauci da rashin kudin da yake fama dashi amma abokansa basu taba daukan abin da gaske ba.

KU KARANTA: Akwai yiyuwar a janye takunkumin shigo da motoci ta bodar kasa - Shugaban Kwastam

Wata abokiyarsa wacce aka sakaye sunarta tace: "A kwanan nan ya kasance yana fada min zai kashe kansa idan bai fita daga cikin talauci ba, amma ban taba tunanin da gaske yake ba."

"Na tuna lokacin da ya kawo min ziyara Jega, yana ta kukan rashin kudi kuma na kan bashi kudin motan komawa Birnin Kebbi; sai yace min idan abubuwa basu canza ba zai kashe kansa."

Ta nuna irin girgizan da tayi lokacin da aka kirata daga Sokoto cewa Benedict ya kashe kansa.

Wata abokiyar tasa daban wacce tayi ikirarin cewa sun taba zama unguwa daya da mamacin a Zuru tace irin wannan abun dan'uwansa yayi a shekarun baya.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da wannan labari inda yace matashin ya kashe kansa ne a unguwar Badariyan birnin Kebbi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel