Shugabancin majalisar dattawa: Ndume ya sake magana akan kayen da ya sha a hannun Lawan

Shugabancin majalisar dattawa: Ndume ya sake magana akan kayen da ya sha a hannun Lawan

Sanatan Borno, Ali Ndume, a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni yace ya ajiye lamarin kaye da ya sha a hannun Ahmed Lawan wajen neman kujerar shugabancin majalisa a kefe.

Mista Ndume yayi takara da sabon Shugaban majalisar dattawa, Mista Lawan, a lokacin rantsar da majalisar dattawa ta tara wanda aka gudanar a ranar Talata, 11 ga watan Yuni.

Yayi takara da Mista Lawan, sanatan jihar Yobe, wanda ya samu goyon bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Da yaki jin duk wani rarrashi da aka yi masa domin ya janye, Mista Ndume yace lallai sai yayi takarar wannan kujera. Sai dai ya sha kaye aa hannun Lawan bayan anyi zaben inda ya samu kuri’u 28.

Ndume wanda ya amince da shank aye a ranar Talata, yace bai yi danasanin matakin da ya dauka ba.

A wani jawabi da yayi a ranar Laraba, ya sake Magana akan kayen da ya sha,inda ya nuna “godiya ga dukkanin wadanda suka goyi bayan takararsa na neman shugabancin majalisar dattawa.”

KU KARANTA KUMA: Yawan mutanen da suka mutu a hare-haren yan bindiga a Niger ya tashi zuwa 47

Yace: “Koda dai an samu hawa matsayin ba, sai dai hakan yayi amfani domin ya kara daraja da gaskiya akan tsarin saboda yayi adalci ga dukkanin yan takarar.”

Ndume ya bayyana cewa dalilin takararsa ba wai don ya tozarta shirin bane, a'a kawai so yake ya tabbatar da damokradiyya da yanci a tsarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel