Akwai yiyuwar a janye takunkumin shigo da motoci ta bodar kasa - Shugaban Kwastam

Akwai yiyuwar a janye takunkumin shigo da motoci ta bodar kasa - Shugaban Kwastam

-Akwai yiyuwar gwamnatin tarayya ta janye takunkumin da ta sanya na hana shigowa da motoci ta bodar kasa.

-Hukumar kwastam zata kaddamar da sabon tsarin shigo da kayayyaki ta boda mai anfani da kimmiyar na'ura mai kwakwalwa

Gwamnati ta sanya takunkumin hana shigowa da motoci ta bodar kasa a cikin watan Janairu 2017.

Takunkumin hana shigowa da motocin ta bodar kasa ya biyo bayan haramta shigowa da akayi da shinkafa tun cikin watan Afrilu 2016.

Akwai yiyuwar gwamnatin ta sake duba lamarin bayan an tabbatar da wani sabon tsarin Hukumar ta kwastam ta Najeria da kuma takwararta ta jamhuriyyar Benin na amfani da fasahar na’ura mai kwakwalwa wajen sanar da kayan da zasu shigo ta boda.

Babban kwantirola na hukumar ta kwastam Col. Hammed Ali(rtd) wanda ya samu wakilcin mataimakin kwantrola mai kula da kimmiyar na’ura mai kwakwwalwa na hukumar, Benjamin Aber, a taron masu ruwa da tsaki akan sabbin dubarori, ya bayyana tabbacinsa cewa idan aka samu tabbatar da wannan yarjejeniya tsakanin Najeriya da Benin, to gwamnatin tarayya zata iya daga takunkumin da ta sanya na hana shigowa da wasu kayayyaki ta bodar kasa.

KARANTA WANNAN: Zamfara: Duk sarkin da ya bari aka kashe mutum a masarautarsa zan tsige shi - Matawalle

Ya bayyana cewa dalilin da ya sanya gwamnati ta hana shigowa da motoci ta bodar kasa na da nasaba da rashin samun hanyoyin da zasu taimaka wajen sanin abubuwan da ake shigowa da su.

Wannan tsari na kasashen guda biyu zai sanya a samu aminci da amana akan abubuwan da ake shigowa dasu ta boda wanda wannan amincin ne zai sanya gwamnati ta janye wannan takunkumi.

Ya ce” Da ana shigo da motoci ta bodar kasa amma kwatsam sai gwamnati ta haramta hakan dalili kuwa, ana wahala wajen hana shigo da haramtattun kaya kuma ana rasa rayuka da kudaden shiga ga gwamnati, hakan yasa gwamnati ta mayar da shigo da kaya ta bodar ruwa kawai.

“Idan motocin suka shigo ta bodar kasa, bamu da bayani akan yadda suka shigo kuma takardun bogi sun zama ruwan dare. Wannan takunkumi an sanya shine don a magance wannan aika aika.”

Ya kara da cewa ”Idan muka samu muka tabbatar da wannan amintaccen tsarin, zai taimakawa hukumomin gwamnati ba wai hukumar kwastam kawai ba kuma ya sanya tsaro akan yadda ake shigo da motoci, kuma gwamnati na iya janye wannan takunkumi.”

Ya kuma bada tabbaci cewa duk bata garin wurarenda jami’an tsaro da na hukumar kwastam ke tsayawa don duba kayan da aka shigo dasu, zasu bacce da kansu.

Za a gyara wuraren da ake tsayawa don duba kayayyakin da aka shigo dasu, kada sai an tabbatar da wannan tsarin sannan masu ruwa da tsaki sujo suna korafi.

Ya ce wannan sabon tsari za a kaddamar da shi zuwa 20 ga watan Yuni.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel