Nan ba da dadewa ba, Buhari da Tinubu za su gane El-Rufa'i munafiki ne - Shehu Sani

Nan ba da dadewa ba, Buhari da Tinubu za su gane El-Rufa'i munafiki ne - Shehu Sani

Tsohon sanata, Shehu Sani, ya ce nan ba da dadewa ba, shugaba Muhammadu Buhari da sauran shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), za su gane cewa munafiki ne kuma zasu dandani gubarsa.

Sani wanda yake mayar da martani kan wani magana da El-Rufa'i yayi sanye da hotunan Shehu Sani da Suleiman Hunkuyi, yana yi musu isgili da kuma alfaharin cewa shi yayi sanadiyar faduwarsu a zabe.

Amma a jawabin shafin Facebook, Shehu Sani, ya mayar da martani mai tsawo kan wannan jawabi inda ya caccaki El-Rufa'i.

KU KARANTA: Tirkashi: Wasu mata sun sace jaririya daga zuwa barka a Zariya

Ya ce gazawar El-Rufa'i wajen samun nasara a zaben majalisar gwamnoni ya nuna cewa gwamnan jihar Kasunan ba ya iya cin kowani zabe ba tare da taimakon shugaba Buhari ba.

Ya siffata El-Rufa'i matsayin wanda ke amfani da dama wajen danewa mulki sannan ya yaudari wadanda suka taimaka masa daga baya.

Yace: "Tarihinka mai muni na tsalle daga wannan uban gidan zuwa wani ubangida sanannan abu ne ga dukkan yan Najeriya. Kuma ina da imanin cewa nan da lokacin kadan shugaba Muhammadu Buhari zai dandani gubarka."

"Kafin na fita daga APC, na fadawa shugaba Buhari, Oshiomole da Tinubu cewa za ka zagesu, za ka yaudaresu kuma za ka yakesu. Wannan na cikin jininka."

Tsohon dan majalisan ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya tsakanin 2015 da 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel