Majalisar tarayya zata sanar da sunayen yan kwamiti a yau

Majalisar tarayya zata sanar da sunayen yan kwamiti a yau

- Ana tsammanin a sanar da kwamitiocin Majalisun tarraya guda uku

- Majalisun tarayya zasu dage zamansu har sai 20 Yuni, 2019

Akwai yiyuwar shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da kakakin majalissar wakilai Femi Gbajabiamila su sanar mambobin kwamiti uku a yau.

Ana kuma tsammanin zasu dage zaman majalisar har sai zuwa Yuni 20, na wannan shekarar.

Bincike ya nuna yan majalisun zasu koma gida bayan zaman da zasu yi yau saboda ba a gama shirya ofishoshinsu ba.

KARANTA WANNAN: Bagudu ya ki tabbatar dani a matsayin Alkalin Alkalai saboda ni kirista ce, inji Alkalin Alkalai

Anyi kokarin a tuntubi babban jami’in yada labarai na majalisa, Rawlings Agada amma hakan yaci tura.

Wani babban dan majalisa wanda ya bukaci a sakaya sunanshi ya ce “Shugabancin jam’iyyar APC da na PDP zasu tura sunayen yan takarkarunsu na mukamin mayan shuwagabannin majalisa.

“Ana tsammanin shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai zasu kafa kwamitin dokoki da ayyukan majalisa, kwamitin yada labarai na wacen gadi, da kwamitin bukatun majalisa.

Alal misali, kwamitin bukatun majalisa shine zai tabbatar da an baiwa yan majalisu kudin da suke bukata don wasu bukatunsu musamman wajen zama. Yan majalisun kuma zasu samu yan wannan kwamiti don a samar masu da dukkan abunda suke bukata na aiki a ofisoshinsu.”

ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel