INEC, APC, lantarki da sauran abubuwan da Buhari yayi magana a kai jiya

INEC, APC, lantarki da sauran abubuwan da Buhari yayi magana a kai jiya

A jiya 12 ga Watan Yuni, 2019, ne aka yi bikin murnar tunawa da damukaradiyya a Najeriya. Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jawabi domin murnar cika shekaru 20 da wanzuwar mulkin farar hula a kasar.

Mun kawo kadan daga cikin wasu manyan abubuwan da shugaban kasar ya fada a wannan rana mai muhimmanci:

Ga wasu kadan daga cikin batun da shugaba Buhari ya taba, wanda ya kamata kowa ya ji:

1. INEC

Shugaban kasa Buhari ya ce ya na ganin kokarin da hukumar zabe mai zaman kan-ta watau INEC ta ke yi na gudanar da zabe. Shugaban kasar ya ce zai dage wajen ganin hukumar ta samu duk kayan aikin da ta ke bukata wajen shirya zabe na kwarai.

2. APC

Shugaban kasar ya kuma godewa duk wadanda su ka yi wa jam’iyyarsa ta APC mai mulki aiki a zaben da ya gabata, a cikin jawabinsa. Buhari ya kuma jinjinawa wadanda su ke tare da shi tun lokacin da ya fara fitowa takara a lokacin zaben 2003.

KU KARANTA: Buhari da Mai dakinsa tare da manyan Shugabannin Afrika a wajen liyafa

3. Najeriya

Shugaba Buhari a jawabin na sa, ya bayyana cewa Najeriya babbar kasa ce a Duniya. Shugaban na Najeriya ya nakalto hasashen da majalisar dinkin Duniya na UN ta yi, na cewa nan da shekarar 2050, za a samu mutane fiye da miliyan 400 a kasar nan.

4. Afrika

Buhari ya kuma bayyana irin kokarin da Najeriya ta saba yi a Afrika na ganin wanzar da zaman lafiya a sauran kasashen Nahiya. Daga cikin kasashen da Najeriya ta ke taimako da soji akwai irin su Gambiya, Zimbabwe, Mozambique, Namibia, dsr.

5. Abubuwan more rayuwa

Shugaban na Najeriya ya kuma bayyana cewa akwai bukatar a yi maza a gyara tituna, da dogon jirgin kasa da sauran hanyoyin ruwa na kasar domin su yi daidai da zamani. Haka zalika akwai bukatar a inganta lantarki a Najeriya inji Buhari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel