Yaki da rashin gaskiya: Za mu fara bi ta kan Ma’aikata da Lauyoyi - Buhari

Yaki da rashin gaskiya: Za mu fara bi ta kan Ma’aikata da Lauyoyi - Buhari

Mun samu labari a Ranar 11 ga Watan Yuni, 2019, cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daga yanzu za ta fara hukunta ma’aikatan da aka samu da laifin rashin gaskiya da rashawa a kasar nan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da bakinsa ya ce gwamnatin tarayyar Najeriya ba za ta rika kyale ma’aikatan da aka samu da laifin satar dukiyar al’umma da rashin gaskiya, su tafi a haka ba.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana, shugaban kasar ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke wani jawabi a taron da hukumar EFCC ta shirya a game da yaki da rashin gaskiya Ranar Talata.

KU KARANTA: Ashe ba da gaske Buhari ya ke fada da Barayin Gwamnati ba

Shugaban kasar ya gabatar da jawabinsa ne a wajen wannan taro da aka shirya domin tattauna yadda za ayi maganin rashin gaskiya da wawurar dukiyar Talakawa musamman a wajen zabe.

Shugaba Buhari ya ce ana ganin nasara a gwamnatinsa, sannan ya tabbatar da cewa daga yanzu Lauyoyi, da ma’aikatan banki da ‘yan kasuwan da aka samu da laifi zai gamu da fushin hukuma.

Muhammadu Buhari ya bayyana yadda gwamnatinsa ta ke kawo sauyi wajen yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa a wajen wannan taro wanda shugaban kasar Tanzaniya ya halarta.

A wajen taron, shugaban hukumar EFCC na kasa, Ibrahim Magu, ya yi jawabi inda ya bayyana cewa a shekarar 2019 kurum, sun yi nasarar kama mutane fiye da 400 da laifi a kotu a Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel