Dole ne mu yiwa talauci kaura daga Najeriya - Tinubu

Dole ne mu yiwa talauci kaura daga Najeriya - Tinubu

Babban jigo na jam'iyyar mai ci ta APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya ce ci gaba da ta'azzarar ta'addancin 'yan baranda, masu garkuwa da mutane, fashi da makami da kuma rikicin makiyaya da manoma ya janyo daduwar talauci a fadin kasar nan.

Tinubu wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Legas ya bayyana hakan cikin birnin Legas yayin gabatar da jawaban sa na bikin sabuwar ranar dimokuradiyya da aka gudanar a ranar Laraba 12, ga watan Yuni.

Cikin kalami na sa, kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar ta APC kuma ya kasance tsohon gwamnan jihar Legas a tsakanin 1999 zuwa 2007, ya ce dole ne a shimfida matakai da za su kawo karshen katutun talauci a kasar nan.

A yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauya ranar dimokuradiyar kasar nan daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni, Tinubu ya ce dole ne a mike tsaye wurjanjan domin ganin al'ummar Najeriya sun ci gaba da kwankwadar romon dimokuradiya ta hanyar yaye talauci da ya yi masu shinge.

KARANTA KUMA: ASUU ta koka da gazawar gwamnati a kan rashin kula da harkokin ilimi

Kazalika tsohon gwamnan jihar Legas ya gargadi al'ummar Najeriya a kan kada su manta cewa jin dadin dimokuradiya da suke yi a halin yanzu sadaukarwar magabata ce da suka bayar da jinin su da kuma rayuka wajen tabbatar da ci gaban kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel