ASUU ta koka da gazawar gwamnati a kan rashin kula da harkokin ilimi

ASUU ta koka da gazawar gwamnati a kan rashin kula da harkokin ilimi

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU, ta yi babatu na bayyana koken yadda shugabanni da kuma jagororin kasar nan suka yi watsi da harkokin ilimi tun daga matakin sa na farko a makarantun firamare ya zuwa na jami'a.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya yi Allah wadai dangane da yadda abubuwa suka tabarbare a kasar nan sakamakon gazawar gwamnati da kuma dabi'ar nuna ko in kula ta shugabanni.

Furucin shugaban ASUU na zuwa ne yayin ganawa da manema labarai a birnin Fatakwal na jihar Ribas dangane da halin da kasar nan take ciki musamman gazawar gwamnatin da kuma shugabanni ta fuskar rashin mayar da hankali a kan harkokin ilimi.

Bayan hikaito yadda gwamnati ke wulakantar da harkokin ilimi a kasar nan, shugaban na ASUU ya kuma buga misali da yadda gwamnatin ke ci gaba da habaka tattalin arzikin wasu kasashen duniya a fannin ilimi wajen malalar dukiyar kasar nan a makarantun kasashen ketare.

Shugaban na ASUU ya zayyana wasu munanan ababe da suka yiwa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari dabaibayi tun bayan nasarar sa ta lashe babban zaben kasa da aka gudanar a shekarar 2015 sabanin yadda aka yi hasashe.

KARANTA KUMA: Osinbajo ya karbi bakuncin tawagar wakilan kasar Indiya a fadar Villa

Jerin munanan ababe da suka mamaye gwamnatin shugaban kasa Buhari kamar yadda Farfesa Ogunyemi ya wassafa sun hadar da matsin tattalin arziki, ta'azzarar katutu na talauci, mafi kololuwar rashin tsaro, rikicin makiyaya da manoma, rikicin addini da kabilanci da kuma annobar garkuwa da mutane.

A baya kungiyar ASUU ta bayyana takaicin yadda gwamnatin Tarayya ta gaza cika alkawarin ta na biyan alawus din malaman jami'o'i bayan yarjejeniyar da suka kulla a tsakanin su da tayi sanadiyar janye yakin aikin sai mama-ta-gani da ta afka a bara.s

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel