Buhari ya karbi bakuncin sabbin shugabannin majalisar wakilai

Buhari ya karbi bakuncin sabbin shugabannin majalisar wakilai

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin sabbin shugabannin majalisar wakilai da aka zaba ranar Talata.

Sabon shugaban kakakin majalisar wakilai, Honarabul Femi Gbajabiamila, da mataikinsa, Honarabul Idris Wase, sun ziyarci shugaba Buhari a fadarsa a daren ranar Laraba. Shugabannin sun samu rakiyar Honarabul Abdulmumin Jubrin, dan masalisar wakilai daga mazabar Kiru/Bebeji a jihar Kano.

Kafin ya lashe zaben kujerar shugaban majalisar wakilai a yau, Talata, 11 ga watan Yuni, Gbajabiamila ya kasance shugaban masu rinjaye a zauren majalisar tun shekarar 2015.

Gbajabiamila, zabin jam'iyyar APC da fadar shugaban kasa, ya samu kuri'u 281 da suka bashi nasara a kan babban abokin hamayyarsa, Umar Mohammed Bago, dan jam'iyyar APC, wnda ya samu kuri'u 76.

Buhari ya karbi bakuncin sabbin shugabannin majalisar wakilai

Buhari da Gbajabiamila
Source: Twitter

Buhari ya karbi bakuncin sabbin shugabannin majalisar wakilai

Buhari da Wase
Source: Twitter

Tun kafin a kammala kidayar kuri'u Bago ya mike tare da zuwa wurin Gbajabiamila domin taya shi murnar samun nasarar lashe zaben kujerar kakakin majalisar wakilai.

Wannan ita ce haduwa ta farko tsakanin shugaba Buhari da shugabannin majalisar bayan samun nasarar su a zaben da aka yi a zauren majalisar ranar Talata, 11 ga watan Yuni.

A gana wa ta karshe tsakanin bangaren zartar wa da shugabancin majalisa da aka yi cikin azumi a fadar shugaban kasa, shugaba Buhari ya ce bai ji dadin mulki da majalisar da Saraki da Dogara suka jagoranta ba.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun bankado wani kamfanin kera bindigu a kudancin Najeriya

A wata hira da aka yi da shi kai tsaye a gidan Talabijin na kasa (NTA), wacce sauran kafafen yada labarai suka watsa, Buhari ya ce ba zai saka Saraki da Dogara da majlisar tarayya karo na 8 a cikin 'yan kishin kasa ba.

Ana ganin wannan karon Buhari ba samu matsala da majalisa ba, musamman wajen zartar da kasafin kudi a kan lokaci da kuma tabbatar da mutanen da shugaban kasa ya bawa mukamai da ke bukatar sahalewar majalisa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel