An ci Kano Pillars tarar Naira miliyan takwas

An ci Kano Pillars tarar Naira miliyan takwas

Hukumar da ke kula da wasan kwallon kafa a Najeriya sun hukunta kungiyar kwallan kafa ta Kano Pillars saboda abinda yan wasan da magoya bayansu sukayi a ranar Litinin.

Babban jami’in hukumar Salihu Abubakar ya ce hukuncin ya biyo bayan tarzomar da aka tayar da cin mutuncin da aka yima alkalan wasan.

Magoya bayan kungiyar Kano Pillars ne da yan wasanta suka aikata laifin a ranar wasa na hudu da aka buga a legas.

An ci Kano Pillars tarar Naira miliyan takwas, kuma an dakatar da mai dora kambunsu Rabi’u Ali daga buga wasanni 12” inji Abubakar.

Kamfanin Dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa magoya bayan kungiyar Kano Pillars sun mamaye filin wasan kuma sun lalata katangu da allunan tallace tallace.

KARANTA WANNAN:Atiku yayi dai-dai da ya kalubalanci nasarar Buhari - Jonathan

Magoya bayan sun kuma yi jefe jefe a a wajen zaman manyan baki. A karshe an tashi kunnen doki tsakanin Kano Pillars da Ranger International 1-1.

Hukumar ta caji Kano Pillars da laifuffuka guda hudu na karya dokokin NPFL.

An caji Ali da laifin cin zarafin alkalin wasan wanda hakan ne ya sanya sauran yan wasan da magoya bayansu suka tada hargitsi da karya dokoki.

Ita kuma kungiyar, an caje ta ne da laifin rashin gudanar da yan wasan ta wanda hakan yasa suka ci zarafin alkalan wasan.

Haka zalika, an umurci kungiyar da su buga wasanninta uku masu zuwa da za tayi a gida ba tare da magoya bayanta sun halarci wasan ba.

Haka kuma, kungiyar zata rasa maki uku a saban kakar wasanni na 2019/2020 idan aka sake samunta da laifi irin wannan.

Dokokin hukumar sun ba kungiyar damar da su karbi hukuncin ko kuma su daukaka kara cikin awa 48.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel