Mun kashe sama da Naira biliyan 14 don hako ma'adanai- Gwamnatin tarayya

Mun kashe sama da Naira biliyan 14 don hako ma'adanai- Gwamnatin tarayya

-Gwamnatin tarayya ta ce ta kashe kudi sama da naira biliyan 14 don hako ma’adanai a cikin shekaru uku.

-Matasa zasu samu aikin yi idan aka bunkasa harkar hako ma'adanai

Tsohon ministan albarkatun kasa Honarabul Abubakar Bawa-Bwari ne ya bayyana haka a wani biki da aka shirya don karrama shi a ministirin da ke Abuja.

Abubakar Bwari ya bayyana cewa ana cigaba da aikin hako ma’adanan kuma ya bukaci duk wanda zai gaje shi da ya dabbaka ayyukan da yayi na ci-gaba.

Ya ce duk da cewa ya gamu da kalubale masu yawa sadda yana ofis musamman matsalar isassun kudi, ministirin karkashin jagorancinshi ta gano wasu muhimman albarkatu da ya kamata gwamnati ta tattala su.

Ya ce hakan zai karawa gwamnati kudaden shiga masu yawa kuma ya samar da aikin yi ga matasa masu zaman banza.

Ya kamata su dabbaka wannan cigaba musamman na hako da ma’adanan. Muna bukatar samun isassun bayanai da kididdiga don samun tabbaci akan yawan ma’adanan. Idan akayi hakan, za a jawo hankalin yan kasuwa saboda zamu san yawan kudin da muke bukata don hako da ma’adanan, muna bukatar manyan yan kasuwa.

KARANTA WANNA: 'Yan sanda sun bankado wani kamfanin kera bindigu a kudancin Najeriya

Ya kara da cewa “Amma yan kasuwan baza su zo ba har sai mun samu tabbataccen bayani. Hakan yasa muke da bukatar samun wannan bayanan, idan aka samu zasu zo kuma za a samu cigaba wajen habbaka tattalin arzikin kasa kuma matasa zasu samu aiki kuma aikin hako ma’adanan zai gudana cikin yanayi mai kyau da kwarewa.”

Cikin manyan bakin da suka halarci bikin sun hada da tsohon kakakin majalissar tarayya Gali Umar Na’abba da babban sakataren ma’aikatar malam Abdulkadir Mu’azu.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel