A karo na biyu: Ndume ya sake yin magana a kan kayen da Sanata Lawan ya yi masaa

A karo na biyu: Ndume ya sake yin magana a kan kayen da Sanata Lawan ya yi masaa

A ranar Laraba ne sanatan jihar Borno, Ali Ndume, ya ce ya saka maganar batun faduwa zaben neman kujerar majalisar dattijai a bayansa.

A wani jawabi mai dauke da sa hannun kakakinsa, Mohammed Alfa, Sanata Ndume ya yi magana a kan kayan da ya sha a hannun sanata Ahmed Lawan tarevda mika godya ga dukkan wadanda suka nuna goyon baya a gare shi.

"Duk da ban samu nasara ba a zaben da aka yi ranar Talata, tsayawar da nayi kadai ta kara wa zaben armashi da mutunci, sannan kuma an yi adalci ga dukkan 'yan takara," a cewar Ndume.

Jam'iyyar APC ta dade da bayyana cewar Lawan ne dan takarar da take so a zaba a matsayin shugaban majalisar dattijai.

A zaben da aka gudanar a ranar Talata, Ndume ya samu kuri'u 28, yayin da Lawan ya samu kuri'u 79.

Da yake magana jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben, Ndume ya ce mutuncin jam'iyyar APC zai shiga tsaka mai wuya da a ce bai yi takara da Lawan ba.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun bankado wani kamfanin kera bindigu a kudancin Najeriya

"Babu dimokardiyya a duk inda babu 'yan takara. Hakan ne yasa na tsaya tsayin daka a kan takara ta. Sashe na 50 (1) na kundin tsarin mulki ya bawa Sanatoci damar zaben shugaban majalisar dattijai da mataimakinsa, kuma hakan ce ta faru a zauren majalisar," a cewar Ndume.

Ndume ya taya Lawan murna tare da yi masa fatan alheri a cikin shekaru hudu da zai yi yana jagorantar majalisar dattijai tare da bayyana cewar Sanatoci tamkar 'yan uwan juna ne da ke da kyakyawar alaka da fahimtar juna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel