Zuciya: Makiyayi ya girbe kan matarsa, ya fada komar 'yan sanda

Zuciya: Makiyayi ya girbe kan matarsa, ya fada komar 'yan sanda

Rundunar 'yan sanda a jihar Ekiti ta tabbatar da kama wani makiyayi a garin Ilasa Ekiti da ke karamar hukumar Ekiti ta gabas a jihar Ekiti, bisa zarginsa da fille kan wata mata da ake kyautata zaton matarsa ce.

Da yake tabbatar da faruwar hakan, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Caleb Ikechukwu, ya ce an kama makiyayin kuma tuni an fara bincike a kan lamarin.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar makiyayin (wanda aka boye sunansa) ya fille kan matar ne a yayin da ta je debo ruwa a wata korama da ke Ilasa Ekiti.

Mutumin ya yi kwanton bauna tare da kai wa matar, wacce suka fito daga kabila daya, hari a yayin da ta je debo ruwa kamar yadda kanwarta wacce abin ya faru a kan idonta ta fada.

Makiyayin ya datse kan matar ne a daidai lokacin da ta durkusa domin kamfatar ruwa daga koramar, sannan kuma ba tare da bata lokaci ba ya cika wandonsa da iska.

DUBA WANNAN: A karo na biyu: Ndume ya sake yin magana a kan kayen da ya sha a hannanun Sanata Lawan

An kama shi ne bayan kanwar marigayiyar da abin ya faru a kan idonta ta bayar da bayanin abinda ya faru ga 'yan sanda.

NAN ta rawaito cewar an fara samun matsala tsakanin makiyayin da matar a cikin watan da ya gabata bayan ta ki amincewa ta zo don yin sallah a gidansa duk da kasancewar an yi musu baiko tun tana matashiya.

Marigayiyar ta shiga gudun Makiyayin tare da kin duk wani shirin yi musu biki bayan ta yi korafin cewar yana shan giya da tu'ammali da miyagun kwayoyi.

A cewar NAN, Makiyayin ya kashe matar ne bisa haushin cewar ita da iyayenta na kokarin ganin ba a yi bikinsu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel